
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta ce ta fara biyan jimillar Naira biliyan 18 na haƙƙoƙin tsofaffin ma’aikatan tsohon kamfanin jiragen sama na Nigeria Airways su guda 2,700, bayan sama da shekaru 20 da rufe shi.
Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattali, Taiwo Oyedele ne ya bayyana haka yayin ganawa da ‘yan jarida a Abuja, ranar Juma’a. Oyedele ya ce, an riga an biya tsoffin ma’aikata guda 2,100 a rukuni daga na ɗaya zuwa bakwai, yayin da sauran ma’aikata 600 na rukuni na takwas da na tara an tantance su a matsayin waɗanda ba sa cikin masu samun wani kaso na kuɗaɗen.
“A jimillance, wannan ya wakilci Naira biliyan 18 aka biya tsofaffin ma’aikatan su 2,700,” inji shi.
Ministan ya bayyana cewa, wasu daga cikin ma’aikatan sun tsufa suna jiran haƙƙinsu, yayin da wasu sun rasu, inda iyalansu suka wakilci su wajen karɓa. Ya ce, wannan mataki ya biyo bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu na a tabbatar da warware bashin da ma’aikatan suke bi sakamakon hidimar da suka yi wa kamfanin da ma ƙasa baki ɗaya.
A cewarsa, duk da cewa kuɗaɗen da aka biya ba sa wakiltar sama da shekaru 20 na jiran, gwamnatin ta ɗauki hakan a matsayin wajibi na warware abin da ta gada a madadin barin su su cigaba da zama har zuwa wani zamani.
Ya ƙara da cewa, sai da aka bi matakai na zamani wajen tantance ma’aikatan ciki har da ɗaukar hoto duba sahihancin bayanan banki da sauransu domin ƙaurace wa iƙirarin damfara daga wasu daga cikin su.
