Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Tarayya ta haramta shiga da katako, gawayi da sauran ire-irensu.
Ministan Muhalli Balarabe Abbas Lawal ya sanar da haka a taron muhalli na ƙasa a Katsina.
Da yake miƙa kundin dokar da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sanya wa hannu ga mataimakin gwamnan jihar, ministan muhalli Balarabe Abbas ya yi fatan gwamnatin jihar da haɗin gwiwa na sashin shari’a za su fitar da dokar da zai samar da masu kula da dazukan jihar.
Mataimakin gwamnan jihar Alhaji Farouk Lawal Jobe wanda ya wakilci gwamnan jihar ya tabbatar wa ministan cewa gwamnati zata hada Kai da majalisar dokokin jihar wajen samar da dokokin da zai karfafa dokar da shugaban kasa ya sanya wa hannu.
Ministan Muhallin ya yaba wa ƙoƙarin gwamnatin jihar na magance yawan ba haya a waje wanda hakan ya sa jihar da take na 24 ta koma zuwa na ɗaya wajen magance lamarin.
Taron Majalisar Muhalli ta ƙasa da ya ɗauki kwanaki uku ya gudanar a Katsina ya ƙunshi Ministan Muhalli da manyan jami’an ma’aikatar da kwamishinonin muhalli na jihohin ƙasar da ƙungiyoyin bada tallafi na ƙasashen waje.
