Gwamnatin Tarayya ta kuɓutar da malaman da aka sace a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jami’an ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), tare da haɗin gwiwar rundunar ‘yan sandan Najeriya, a ranar Juma’a sun kuɓutar da uku daga cikin malamai shida da aka sace a Jihar Zamfara.

An sace malaman ne a ranar 12 ga Satumba, 2026, da misalin ƙarfe 11:30 na safe, a kan hanyar Dakko-Damri kusa da Dajin Sububu da ke ƙaramar hukumar Bakura.

Rahotanni sun bayyana cewa malaman na kan hanyar zuwa Talata Mafara ne domin halartar zaman addu’a na musamman da aka shirya wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, lokacin da ‘yan bindiga ɗauke da makamai suka tare su a Gidan Suleiman Bature, kimanin kilomita uku daga ƙauyen Damri.

Malamai da aka sace ɗin sun haɗa da Imam Yahuza, Magawata Abdullahi, Malam Shehu Dakko, Imam Bala Fagon, Na’ibi Tasi’u da wani mutum ɗaya.

Masu garkuwan sun buƙaci a biya kudin fansa na Naira Miliyan 30.

Babban jami’in tsaro da ya halarci aikin ceto sun ya tabbatar a Gusau cewa an kuɓutar da malaman ukun ba tare da sun ji rauni ba, bayan wani samame da aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri.

Ya ce waɗanda aka kuɓutar sun riga sun yi gwajin lafiya da kuma tantancewar tsaro, kuma suna cikin ƙoshin lafiya, ana jiran miƙa su a hukumance ga Gwamnatin Jihar Zamfara domin su koma ga iyalansu.

Da yake tabbatar da ceto din, Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Zamfara, CP Ahmad Muhammad Bello, ya yaba da haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro da ya kai ga nasarar aikin.

CP Bello ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da samame, tare da goyon bayan sahihan bayanan sirri daga al’ummomin yankin, domin kuɓutar da ragowar mutum ukun da kuma cafke wadanda suka aikata laifin.

Ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da goyon baya ta hanyar bayar da sahihan bayanan sirri a kan lokaci domin taimakawa yaƙi da ‘yan bindiga da sauran miyagun laifuka a jihar.

By ukarofi

Leave a Reply