Gwamnatin Tarayya ta wajabta gwajin miyagun ƙwayoyi kan ɗaliban sakandare

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaddamar da sabbin tsauraran matakai domin yaƙi da shaye-shaye da amfani da miyagun ƙwayoyi a makarantu, inda ta wajabta gwajin ƙwayoyi ga ɗaliban makarantun sakandare tare da tanadin dakatar da ɗaliban da aka samu suna ci gaba da amfani da ƙwayoyi bayan shan magani da gyaran hali.

Rahoton ya nuna cewa sabbin matakan na ƙunshe ne a cikin Jagororin ƙasa Na Yaƙi Da Amfani Da Miyagun ƙwayoyi A Makarantu A Nijeriya, wanda aka tsara domin rage yawaitar shaye-shaye tsakanin ɗalibai da kuma samar da yanayin karatu mai aminci a makarantun faɗin ƙasa.

Bisa ga sabon tsarin, duk sabon ɗalibin da zai shiga makarantar sakandare zai fuskanci gwajin ƙwayoyi na tilas kafin a karɓe shi makaranta.

Takardar ta bayyana cewa manufar tsarin ita ce samar da yanayi mai kyau na koyarwa da koyo ta hanyar rage illolin da shaye-shaye ke yi ga lafiyar kwakwalwa da kuma sakamakon karatun ɗalibai.

Haka kuma, an umurci makarantu da su riƙa gudanar da gwajin ƙwayoyi lokaci zuwa lokaci, ciki har da gwaje-gwajen bazata, ga sabbi da tsofaffin ɗalibai aƙalla sau ɗaya a kowace shekara ta karatu.

Sabon tsarin ya haramta wa ɗalibai mallaka ko amfani da miyagun ƙwayoyi, sinadarai masu sa maye ko wasu ƙwayoyin da ba su da izinin hukumomin makaranta.

Sai dai gwamnatin ta ce ɗaliban da ke amfani da wasu magunguna saboda larurar lafiya dole ne iyayensu ko masu kula da su su bayyana hakan lokacin neman gurbin karatu.

Tsarin ya kuma tanadi matakai uku na kula da ɗaliban da aka samu suna amfani da miyagun ƙwayoyi.

A mataki na farko, ɗalibin da aka samu da laifi zai samu shawara da kulawar farko daga makaranta. Idan aka sake samun sa a karo na biyu, za a tura shi wurin ƙwararrun likitoci ko masana domin samun kulawa ta musamman.

Amma idan aka sake kama ɗalibin a karo na uku bayan matakan gyara, tsarin ya ce za a dakatar da shi na ɗan lokaci daga makaranta domin ci gaba da jinya da gyaran hali.

Jagororin sun kuma wajabta ba ɗalibai shawarwari kafin da bayan gwajin ƙwayoyi domin rage fargaba da taimaka musu wajen fahimtar sakamakon gwajin.

Haka kuma, an umurci kowace makaranta da kafa kwamitin ladabtarwa ƙarƙashin jagorancin shugaban makaranta domin kula da aiwatar da dokokin.

Takardar ta ƙara da cewa, duk wani rikici ko tashin hankali da ya samo asali daga amfani da miyagun ƙwayoyi, ciki har da faɗa ko raunata mutane, dole ne a kai rahoto ga jami’an tsaro.

Bugu da ƙari, tsarin ya tanadi cewa duk ɗalibin da ya ƙi bin tsarin jinya ko gyaran hali za a ware shi daga makaranta har sai an tabbatar da cewa ya samu sauƙi.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan ƙaruwar shaye-shaye tsakanin matasa a Nijeriya, lamarin da masana ilimi da lafiya ke cewa yana lalata tarbiyya, sakamakon karatu da lafiyar kwakwalwa.

Sai dai yayin da wasu ke ganin matakin zai taimaka wajen rage shaye-shaye a makarantu, wasu na nuna damuwa kan yadda za a aiwatar da tsarin da kuma ko makarantu da cibiyoyin lafiya suna da isasshen ƙarfin gudanar da shi yadda ya kamata.

A wani ɓangaren kuma, Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta ƙasa (JAMB) ta sanar da cewa za ta gudanar da taron tsara manufofin shekarar 2026 a yau Litinin, inda za a yanke muhimman shawarwari kan tsarin bayar da guraben karatu a jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi.

Mai Ba Hukumar Shawara Kan Hulɗa Da Jama’a, Fabian Benjamin, ya bayyana cewa Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne zai jagoranci taron, wanda zai haɗa masu ruwa da tsaki a fannin ilimi domin tantance mafi ƙarancin makin shiga manyan makarantu na shekarar 2026.

JAMB ta kuma bayyana cewa tawaga daga ƙasar Saliyo za ta halarci taron domin nazarin yadda tsarin bayar da guraben karatu na Nijeriya ke aiki, yayin da ƙasar ke duba yiwuwar kafa irin wannan tsari.

By ukarofi