Kungiyar masu sayar da kayan gyaran motoci ta sha alwashin samar da cigaba — Baban Uwani

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Sabon shugaban ƙungiyar masu sayar da kayan gyaran ababen hawa ta jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ahmad Baban Uwani, ya sha alwashin kawo gyara da cigaba a harkokin kasuwancin ƙungiyar.

Ya bayyana hakan ne yayin bikin rantsar da sabbin shugabannin kungiyar da aka gudanar a dakin taro na tunawa da Malam Aminu Kano da ke unguwar Gwammaja a Kano.

Kungiyar, wadda aka fi sani da Kano State ɓehicle Spare Parts Sellers Association, ta gudanar da zaben shugabanninta ne ta hanyar maslaha domin jagorantar kungiyar na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

A jawabinsa, shugaban ƙungiyar ya ce za su mayar da hankali wajen tsaftace harkokin kasuwanci, ƙarfafa haɗin kai tsakanin ‘yan ƙungiyar da kuma tabbatar da zaman lafiya domin bunƙasa harkokin kasuwanci.

Ya yaba wa hukumomi, ‘yan kasuwa da abokan hulda bisa irin fahimtar juna da zaman lafiya da ake samu a kasuwannin jihar Kano.

Haka kuma ya yi addu’ar samun zaman lafiya da karin arziki ga ‘yan kasuwa da al’ummar Kano baki ɗaya.

By ukarofi