Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta fara tattaunawa da Bankin Duniya kan neman sabbin rance uku da jimillar kuɗinsu ta kai Dala biliyan 1.5, a daidai lokacin da jimillar bashin Nijeriya ya haura zuwa matakin da ba a taɓa gani ba, inda ya kai Naira tiriliyan 166.79 a ƙarshen watan Yuni 2026.
Sabbin rancen sun ƙunshi dala miliyan 500 kowanne, waɗanda aka tsara domin tunkarar sauyin yanayi, ƙarfafa tsarin tallafa wa marasa galihu da kuma bunƙasa harkokin yara ƙanana.
Bayanan ayyukan Bankin Duniya sun nuna cewa mafi kusa da fara aiwatarwa daga cikin shirin shi ne ƙarin dala miliyan 500 da aka nema domin aikin ƙarfafa Jure Sauyin Yanayi a Yankunan Filayen Hamadar Sahel (ACReSAL).
Ana sa ran Bankin Duniya zai duba batun wannan ƙarin kuɗaɗe a ranar 29 ga Oktoba, 2026, yayin da Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya za ta jagoranci aiwatar da aikin.
Idan aka amince da ƙarin kuɗaɗen, jarin aikin ACReSAL zai tashi daga dala miliyan 700 zuwa dala biliyan 1.2. Za a yi amfani da kuɗin wajen farfaɗo da muhalli, gyaran hanyoyin ruwa, yaƙi da zaizayar ƙasa da ambaliyar ruwa, bunƙasa ban ruwa da magudanan ruwa, dashen bishiyoyi da sauran ayyukan da za su taimaka wajen rage illolin sauyin yanayi.
Bankin Duniya ya ce gwamnatin Nijeriya ta nemi ƙarin kuɗaɗen ne domin faɗaɗa nasarorin da aka samu daga aikin da kuma ƙarfafa tsarin gudanarwa, aiki da kuma samar da kuɗaɗen da ake buƙata domin tabbatar da ɗorewar kula da muhalli a faɗin yankunan da aikin ya shafa.
A halin yanzu, aikin ACReSAL yana gudana a jihohin Arewa 19 da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja (FCT).
Rance na biyu da gwamnatin Nijeriya ke nema shi ne dala miliyan 500 daga ƙungiyar Raya ƙasashe ta Duniya (IDA), wadda ke ƙarƙashin Bankin Duniya, domin shirin ƙarfafa Arzikin Gidaje da Dogaro da Kai – Kariya ga Jama’a (HOPE-SP).
An tsara shirin ne domin samar da tallafin jinƙai na yau da kullum ga iyalai masu ƙaramin ƙarfi da sauran masu fama da matsanancin buƙata, tare da inganta tsarin tallafin jinƙai a matakin gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.
Bankin Duniya ya ce shirin zai samar da ingantaccen tsarin tallafa wa iyalai marasa galihu da masu rauni, wanda a hankali zai dogara da kasafin kuɗaɗen gwamnatin tarayya da jihohi, tare da aiwatar da shi ta ingantattun tsare-tsaren gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi.
Rancen zai taimaka wajen bayar da tallafin kuɗi kai tsaye ga waɗanda aka tantance, sabunta rajistar masu cin gajiyar tallafin jinƙai ta ƙasa, haɗa Lambar Shaidar ɗan ƙasa (NIN) da tsarin bayanan tallafin jinƙai, tare da ƙarfafa hanyoyin aiwatar da shirin.
Ana sa ran za a gudanar da bitar fasaha kan tsarin aikin a ranar 30 ga Oktoba, 2026, yayin da aka tsara ranar 16 ga Maris, 2027 a matsayin ranar da ake sa ran amincewa da shirin.
