Gwamnatin Tarayya ta haramta wa ’yan kwangila samun ayyukanta shekaru biyar

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta amince da sabbin ƙa’idojin dakatar da ’yan kwangila, masu ba da shawara da masu samar da ayyuka daga shiga harkokin kwangilar gwamnati, inda aka tanadi dalilai shida da za su iya sa a hana su shiga ayyukan gwamnatin tarayya na tsawon shekaru uku zuwa biyar.

Sabbin ƙa’idojin sun haɗa da bayar da cin hanci ko wasu alherai domin yin tasiri kan shawarar bayar da kwangila, samun hukuncin laifin damfara, ƙin cika sharuɗɗan kwangila da gangan, tarihin rashin kyakkyawan aiki, gurɓata takardu da kuma kasancewa wata ƙungiya ta ƙasa da ƙasa mai ɓangarori da dama ta dakatar da kamfanin.

Umarnin yana ƙunshe ne cikin wata takarda mai taken “Aiwatar da ƙa’idar ƙasa kan Dakatar da ’Yan Kwangila”, wadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya sanya wa hannu.

An aika da takardar zuwa ga Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Babban Sakataren Shugaban ƙasa, ministoci, Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro na ƙasa, Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Tattalin Arziki, masu ba da shawara na musamman da manyan mataimaka na musamman.

Haka kuma, an aika da ita ga shugabannin rundunonin tsaro da Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, da shugabannin Hukumar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda, Hukumar ɗa’a ta Ma’aikatan Gwamnati, Kotun ɗa’a ta Ma’aikatan Gwamnati, Hukumar Rarraba Ma’aikata ta Tarayya, Hukumar Tattara Kuɗaɗen Gwamnati da Rarraba su, Hukumar Harajin Cikin Gida ta Tarayya da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa.

Sauran hukumomin da aka aika wa takardar sun haɗa da Hukumar ƙidayar Jama’a ta ƙasa, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta da sauran Laifukan da Suka Shafi Hakan, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa, da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa.

Haka kuma, an aika da ita ga dukkan manyan sakatarori da shugabannin sassan gwamnati masu zaman kansu da ma’aikatu, Magatakardar Majalisar Dokoki ta ƙasa, Babban Magatakardar Kotun ƙoli, Akanta-Janar na Tarayya, Babban Odita-Janar na Tarayya, da manyan daraktoci da shugabannin hukumomi da kamfanonin gwamnati.

Akume ya ce, an samar da ƙa’idojin ne domin “inganta gaskiya, bin ƙa’idoji da riƙon amana a harkokin sayen kayayyaki da ayyuka na gwamnati, tabbatar da cewa an samu darajar kuɗin da aka kashe, da kuma kare gwamnati daga ’yan kwangilar da ba su da inganci ko kuma ba sa cika alkawurran da suka dauka.”

By ukarofi

Leave a Reply