Gwamnatin Tinubu ta saka tallafin data ga miliyoyin ɗalibai

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cire kuɗin data ga miliyoyin ɗaliban Nijeriya da ke amfani da wasu manhajoji da kafafen koyarwa da gwamnati ta amince da su, a wani sabon shiri da aka ƙaddamar domin sauƙaƙa wa ɗalibai samun damar karatun zamani ta hanyar intanet.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin ƙaddamar da Shirin Samar da Damar Samun Kafafen Koyarwa da Abubuwan Ilimi Ta Intanet Ba Tare da Kuɗin Data ba a Nijeriya.

Alausa ya ce, shirin, wanda ke ƙarƙashin ajandar Sabunta Fata ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na da nufin kawar da ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke hana yaɗuwar ilimin zamani ta intanet a ƙasar.

Ya ce, manufar shirin ba wai samar da damar shiga intanet kaɗai ba ce, illa dai tabbatar da cewa ɗaliban da ba su da halin biyan kuɗin data su ma za su iya samun ingantaccen ilimi.

“Wannan shiri ya wuce batun samar da hanyar sadarwa. Manufarsa ita ce a kusantar da ilimi ga yara waɗanda wataƙila ba za su iya biyan kuɗin data da ake buƙata domin samun damar karatunsu ba,” inji shi.

Ministan ya bayyana cewa talauci, wurin da mutum yake zaune da kuma ƙarancin kayan more rayuwar ilimi na zamani bai kamata su zama dalilin hana ɗaliban Nijeriya samun damar ilimi ba.

A cewarsa, waya, kwamfuta ko kwamfutar hannu na iya zama aji, ɗakin karatu da kuma hanyar samun damar buɗe wasu damammaki, muddin aka cire kuɗin da ake kashewa wajen samun abubuwan karatu ta intanet.

Shirin na zuwa ne a daidai lokacin da Nijeriya ke fuskantar matsalolin ilimi da kuma tazarar da ke tsakanin masu samun damar amfani da fasahar zamani da waɗanda ba sa iya samun irin wannan damar.

Asusun Tallafa wa ƙananan Yara na Majalisar ɗinkin Duniya, UNICEF, ya sha bayyana cewa miliyoyin yara a Nijeriya ba sa zuwa makaranta, yayin da rashin isasshiyar hanyar sadarwa, wutar lantarki da kuma ƙarancin ilimin amfani da fasahar zamani ke ƙara hana yara, musamman waɗanda ke yankunan karkara, cin gajiyar ilimin fasahar zamani.

Wannan yanayi ya sanya farashi da samun data cikin sauƙi suka zama muhimman abubuwa a ƙoƙarin gwamnati da aungiyoyin ci gaba na amfani da manhajojin intanet wajen ƙara wa tsarin koyarwa na gargajiya ƙarfi.

Nijeriya ta taɓa aiwatar da irin wannan tsarin na cire kuɗin data ga wasu ɓangaren karatu. UNICEF ta bayyana cewa an cire kuɗin data ga masu amfani da Nigeria Learning Passport, ta hanyar ba su damar shiga manhajar ba tare da cin data ba a wasu layukan Airtel, tare da faɗaɗa hanyoyin sadarwa zuwa wasu makarantu da ke yankunan da ke da wahalar samun sabis.

Nigeria Learning Passport wani shiri ne da Gwamnatin Tarayya ta samar tare da haɗin gwiwar UNICEF da sauran abokan hulɗa, domin samar da manhajojin karatu na tsarin manhajar ƙasa ga ɗalibai da malamai, tare da ba da damar ci gaba da koyo ba tare da dogaro da aji na makaranta kaɗai ba.

By ukarofi

Leave a Reply