Gwamnatin Yobe ta ƙaryata kai wa jiga-jigan APC hari a wajen taro

Daga WAKILINMU

Gwamnatin Jihar Yobe, ta ƙaryata labarin da aka yaɗa a wasu kafafen yaɗa labarai cewa an yi wa gangamin yaƙin neman zaɓen Jam’iyyar APC ruwan duwatsu a Ƙaramar Hukumar Gashua da ke jihar.

Darakta Janar na yaɗa labarai ga Gwamnan Yobe, Mamman Mohammed, ya ƙaryata faruwar haka, tare da cewa babu ƙamshin gaskiya a cikin lamarin.

“Gangamin ya samu dubban mahalarta wanda ba taɓa ganin irinsa ba a tarihin siyasar garin Gashua.

“Taron ya yi kyakkyawar tarba ga Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, Gwamna Buni da mambobin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe.

“Gwamna Buni ya ratsa taron zuwa kan dandamali a natse babu wata takura, yayin magiya baya ke nuna masa ƙauna.

“La’akari da tsayuwar dandamalin saboda yawan jama’ar da ke kansa, ya sa Daraka Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC, Sanata Muhammad Hassan, ya dakatar da sauran masu jawabi bayan da Shugaban Majalisar Dattawa ya kammala nasa.

“Daga nan ya unarci kowa da ya sauka daga kan dandamalin gudun kada ya rushe.

“An ci gaba da gudanar da taro har zuwa lokacin da manya baƙi suka tafi, kuma babu wata matsala ta tsaro da aka fuskanta kuma babu wanda aka kai wa hari,” in ji sanarwar.

Mohammad ya ce labarin ƙarya da aka yaɗa sharrin masu neman ɓata kyakkyawar danganatakar da ke tsakanin al’ummar Gashua gwamnatin Jihar Yobe ƙarƙashin APC.