DSS ta gayyaci Fani-Kayode kan zargin juyin mulki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar tsaro ta DSS ta gayyaci jigo a Jam’iyyar APC, Femi Fani-Kayode, kan zargin da ya yi cewa an shirya yunƙurin juyin mulki, kamar yadda jaridar News Point Nigeria ta rawaito.

Fani-Kayode ya ba da sanarwar gayyatar da DSS ta yi masa ne cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar Litinin.

A cewarsa babu abin da yake tsoro, don haka zai amsa gayyatar ba tare da wani haufi ba.

Ya ƙara da cewa, babu abin da zai hana shi ci gaba da bayyana ra’ayinsa muddin yana raye.

Ya ce, “Kwanaki uku da suka gabata, a ranar da na wallafa saƙo a Tiwita game da rahotanni jaridu da suka yi zargin Atiku ya yi ganawar sirri da manyan sojoji.

“Na samu saƙon tes daga wani da ya yi ikirarin jami’in DSS ne inda ya buƙaci in tafi ofishinsu kan batun da ya shafi tsaron ƙasa.

“Ban kula gayyatar ba saboda abu ne mai ruɗani, kuma ba ni da tabbacin saƙon tes ɗin daga DSS ya fito.

“Ko ma dai yaya batun yake, ban yi niyar zuwa ko’ina ba har sai na samu gayyata a hukumance.

“Abin mamaki, kwana biyu bayan haka sai na samu wasiƙar gayyata a hukumance, wato jiya da yamma ke nan.

“Da na ɗaga waya na kira, aka shawarce ni kan in ɗauki batun da muhimmanci sannan in amsa gayyata a rana da kuma lokacin da aka tsayar in ba haka ba lamarin zai tsananta.

“Lamarin ya yi mini daɗi da na fahimci kiran ya fito ne daga ɗaya daga cikin karnukan Atiku kan jami’an tsaro su tsare ni.

“A bayyane yake cewa ba Atiku ne ya turo DSS ba, aikinsu kawai suke yi da suka gayyace ni kan batun da ke buƙatar bayani. Nakan martaba gayyatarsu duk lokacin da suka yi mini ita bisa ƙa’ida saboda wannan shi ne abin da ya dace

“Hakan na da muhimmanci musamman ganin cewa batun ya shafi tsaron ƙasa wanda na ɗauke shi da mhimmancin gaske.

“Ba ni da wani abin ɓoyewa, kuma zan gabatar da kaina ga DSS da safen nan kamar yadda aka buƙace ni,” Fani-Kayode.

A jerin saƙonnin da ya wallafa ran Asabar a shafinsa na Tiwita, Fani-Kayode ya ce ya fahimci ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi wata ganawar sirri da wasu manyan hafsan sojoji.