2023: Babu zaɓe a rumfunan zaɓe 240 – Yakubu

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ce zaɓe ba zai gudana ba a wasu rumfunan zaɓe 240 a faɗin ƙasa a zaɓe mai zuwa.

Shugaban INEC na Ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a wajen ganawarsu da jam’yyun siyasa a ranar Litinin.

A cewar Yakubu, hakan ya faru ne saboda babu wanda ya zaɓi ya kaɗa kuri’a a rumfunan zaɓen da lamarin ya shafa.

Wannan na zuwa ne yayin da ya rage kwanaki 12 kafin baban zaɓen 2023.

A cewar Yakubu babu wanda ya nuna sha’awar kaɗa ƙuri’a a rumfanar yayin rijistar zaɓen da aka yi wa jama’a saboda dalilai na tsaro.

Da wannan, Yakubu ya ce yanzu adadin rumfunan zaɓen da za a kaɗa ƙuri’a sun tashi 176,606.

Shugaban na INEC ya ce a 2021 aka faɗaɗa yawan rumfunan zaɓe bayan cika matakan da suka dace don sauƙaƙa wa jama’a samun rumfunan zaɓe kusa da su.

Ya ce tun bayan ƙarin rumfunan da aka yi a 1996, ba a sake yin wani ƙarin ba sai a 2021.

Wanda hakan ya sa adadin rumfunan zaɓe ya ƙaru daga 119,973 zuwa 176,846 da ake da shi a yanzu.

“Kodayake akwai wasu rumfunan zaɓe 240 waɗanda ba su da masu kaɗa ƙuri’a a tsakanin jihohi 28, ciki har da Abuja.

“Jihohin Taraba da Imo su ne kan gaba, inda suke da rumfuna 34 da 38.”

A cewar shugaban na INEC, hakan ya faru ne biyo bayan babu wanda ya yi rijista a ƙarƙashin rumfunan yayin shirin rijistar masu zaɓe da aka gudanar.