Zaɓen 2023: Aski ya zo gaban goshi!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Azancin zancen Hausawa na cewa aski in ya zo gaban goshi ya fi zafi duk da ba lalle kowa ya kan ji zafi don askin da a ke yi ma sa ya zo goshi ba. Gaskiya ma hakan ya danganta ga wanzamin da ya ke askin. Idan an samu goni ya jika sabulu da ɗan ruwa mai sanya ya shafa ya murza aska sai askin ya yi sanyi kuma har ma a riƙa hira tsakanin wanzamin da wanda a ke yi wa askin.

Shin wannan zaɓen ya na zafi ko ba shi da shi a zahiri dai an samu dogon lokaci tun dawowa dimokraɗiyya a 1999 ba a shiga lamuran zaɓe ba tare da shugaba Buhari yana takara ba. In an tuna a 2003 shugaba Buhari ya fara takara, ya sake takara a 2007 ya maimaita a 2011 inda aka samu fitinar da aka rasa rayuka.

A ƙarshe dai Allah ya ba shi nasara a 2015. Bayan kammala wa’adin farko ya nemi tazarce a 2019 inda hukumar zaɓe ta sake ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓe. Abin da a ke jira shi ne shugaban ya samu damar shaida miqa ragama ga sabon shugaba a ranar 29 ga watan mayu mai zuwa.

Duk da dan takarar jam’iyyar sa ta APC Bola Ahmed Tinubu ya yi zargin ƙarancin mai da canjin kuɗi na zama zagon ƙasa ga nasararsa a zaɓe, hakan bai hana ya ziyarci shugaba Buhari su ka tattauna ba. Hakazalika an ga shugaban a gangamin yaƙin neman zave na APC a Nasarawa ya na buƙatar mutane su zavi Tinubu da ba da shaidar sun kasance tare wajen shekaru 20 kuma Tinubu ya amince da Nijeriya.

A nan dai shugaban bai sauka daga turbar magana ba wajen gugar zana ga ‘yan takarar sauran jam’iyyu sai dai ya tsaya kan bayyana dalilan da ya ke fata ‘yan kasa za su mara baya ga Tinubu. Shugaba Buhari ya ƙara ƙarfafa matsayar da ba mamaki don kwaranye zargin angulu da kan zabo da ake yi wa wasu mutanen sa a fadar Aso Rock ya roƙi mahalarta kamfen ɗin su isar da saƙon ga sauran jama’a a gida.

Ko ma wane zargi za a yi salon shugaba Buhari a shekarar sa ta miƙa mulki ya yi bambanci da irin na Obasanjo da ya zayyana zaɓen 2007 da cewa na ko a yi rai ko a mutu ne. Haƙiƙa a zahiri magoya bayan Tinubu na gani-kashe-ni za su so shugaba Buhari ya riƙa zafafa kalamai na nuna lalle zaɓar Tinubu kaɗai mafita ga Nijeriya kuma ba ma mai iya kada Tinubun.

Gabanin nan ma shugaban ya amsa tambayar da a ka yi ma sa cewa ga wa zai miƙa ragama sai ya ce ga duk wanda ‘yan Nijeriya su ka zaɓa. In mun duba za mu fahimci cewa ba karsashin da a ka saba gani a zaɓukan baya ga babban zaɓen. Kuma maimakon mutane su matsa lamba kan zaɓen, sun fi maida hankali ga ƙalubalen canjin kuƙi da ƙuncin rayuwa.

Ko da wasu na son amfani da ƙabilanci ko vangaranci da sauran rabe-rabe a zaɓen, takaicin rayuwar yau da kullum ta shafi akasarin jama’a don haka kuka ya fi yawa a tsakanin jama’a kuma ba tabbacin akwai wanda kai tsaye zai zo ya sharewa mutane hawaye. In a ka ce min wasu na sanyin gwiwar fitowa ranar zaɓe ba zan yi mamaki ba.

Ga ma raɗe-raɗi ko fargabar ba lalle ne ma a iya gudanar da zaɓen ba don dalilai na zahiri na rashin tsaro a wasu sassa da kuma yadda wasu ‘yan takara su ka buge da cusawa juna kalaman ɓatanci.

Sauyi zai samu ko ba zai samu ba Allah ya bar wa kan sa sani amma ‘yan ƙasa na da damar kawo sauyin. Kuma tabbas sauyi zai iya samuwa ko ba mai ma’ana ba. Yadda a ke samun sauyi mai ma’ana shi ne masu zaɓe su fidda son rai a zaben wajen zaɓen waɗanda su ka cancanta ko da su na da kuɗi ko ba su da shi ko da su na da kyan fuska ko ba su da ita kuma ko da sun fito daga sashen da a ka cusa hamayya tsakaninsa da ɗaya sashen ta hanyar akasin tarihi, bambancin ƙabila ko addini.

In an samu haka sai kuma a yi fatar bugun ƙirji da hukumar zaɓe ke yi cewa ta vullo da na’urar da za ta hana maguɗin zaɓe mai laƙabi da BVAS ta yi aiki wajen tsabtace zaɓen inda wanda jama’a masu rinjaye su ka zava zai zama an ayyana a matsayin wanda ya yi nasara. Hakazalika mutane su kar cijewa su fito zaɓe da kauce wa damuwa da kuɗi ko wata kyauta daga ‘yan siyasa.

Sam-sam ba ra’ayin adalci ba ne a cewa talaka mai zaɓe ya karɓi kuɗi daga ‘yan siyasa masu ba da kuɗi ko dan takara mai ba da kuɗi sannan su zaɓi wani daban. Matuƙar mutum ya karɓi kuɗi da alƙawarin kaɗawa wanda ya ba shi kuɗi baya to ya kaɗa ƙuri’a gare shi shi ne adalci. Kawai kar ma a karvi kuɗin matuƙar ba za a cika alƙawarin zaɓe ba. Za ka ga dan siyasa na cewa in an ba ku kuɗi ku karɓa amma ku zaɓe ni! wannsn ba daidai ba ne. Kuɗi daban zaɓen nagari kuma daban.

Babban ƙalubalen zaɓen nan wataƙila shi ne rashin samun ainihin mutumin da mutane ke so tsakani da Allah. Zai yi kowa na mara baya ga wani ɗan takara don dalilin ƙashin kai da ya haɗa da ƙabilanci, addini ko ɓangaranci.

Hakanan ko kuma don tsammanin samun wata alfarma ko amsar nagoro. A yanayin da aka aza mara baya ga mizanin ƙashin kai a irin ƙasa kamar Nijeriya akwai damuwa ta zaɓen ko wanda za a zavan ba zai aikata abun da ya dace ba. Za ka ga an yi gangami an zaɓi dan takara amma sai a wayi gari gara jiya da yau. Babban abun da kan haddasa hakan shi ne zaɓe bisa dalilan ƙashin kai.

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyu sun fafata a muhawarar zauren VOA;

Masu ruwa da tsaki na manyan jam’iyyun Nijeriya sun fafata a muhawarar zauren VOA da Muryar Amurka ta shirya a Abuja.

Taken muhawar shi ne hasashen ma’abota jam’iyyun kan irin tasirin da su ke ganin su na da shi a zaɓen 2023.

Duk da a lokuta da dama zauren ya hargitse don wani ya ambata wani ra’ayi da ya sava da muradun sauran jam’iyyun, aƙalla dai kowa ya samu damar nuna gwanin sa zai iya lashe zaɓen da za a gudanar a ranar 25 ga watan nan na Febrairu.

Sanata Aliyu Sabi Abdullahi daga Neja ya ce ya na da kyau a mara baya ga dan takarar APC Bola Ahmed Tinubu don hakan ya zama nuna karamci musamman daga yankin Arewa na yanda Tinubun ya mara baya ga shugaba Buhari ya samu ƙarin tagomashin da ya ba shi damar lashe zaɓe a 2015.

Nan take Sabo Imamu Gashua wanda a baya ɗan gani kashenin shugaba Buhari ne, ya ce APC da PDP sun gaza kuma lokaci ya yi da za a gwada Rabi’u Musa Kwankwaso na NNPP don ba ya saba alƙawari kuma ya na damuwa da buƙatun al’ummarsa.

Ɗan kwamitin zaɓen fidda gwani na APC da Tinubu ya lashe Muhammad Saleh Hassan ya ce a gaskiya ba shi da shaidar zargin da a ka yi cewa an yi amfani da kuɗi wajen sayen wakilan zaɓe; amma duk da haka shi ya fi gamsuwa da zaɓen ɗan takarar PDP Atiku Abubakar.

A na sa bayanin jami’in tara kuɗi a ofishin goyon bayan shugaba Buhari BSO Ibrahim Hussaini Abdulkarim ya ce shi tuni ya dawo daga rakiyar APC da ma salon mulkin shugaba Buhari, don haka yanzu ma shi daraktan kamfen ne na ɗan takarar jam’iyyar Leba Peter Obi.

Abdulkarim ya ce zargin da a ke yi wa wasu magoya bayan Obi cewa su na da muradin kafa ƙasar Biyafara ba gaskiya ba ne, kuma ko da gaskiya ne adadin yawan mutanen da a ka kashe a arewa daga miyagu iri daga ‘yan Arewa ya ninninka kisan da miyagun Biyafara su ka yi.

Duk waɗanda su ka halarci zauren sun samu damar bayyana ra’ayin su kan dalilan da su ke ganin gwanayen su ne su ka fi cancantar karɓar ragama bayan kammala wa’adin shugaba Buhari.

Kammalawa;

Tun a na lissafin shekaru zuwa watanni har a ka zo yanzu makonni za a wayi gari da yardar Allah a na cewa yau ne ranar zaɓe. A kyautata niyya a gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali kuma kar a kawo duk wani ruɗani ko da sakamakon bai yi wa wasu daɗi ba.

A zaɓe ko da adalci ko babu a kan samu sakamako don haka a yi amfani da damar tsarin mulki wajen amincewa ko bin kadun abun da ba a gamsu da shi ba.

Dimokraɗiyya dai kamar yanda a ke cewa zaɓin jama’a ne amma ba a kowa ne lokacin jama’a kan samu abun da su ke so ba, kuma su ma ba kowa ne lokaci su ka dacewa su zaɓi wanda ya dace ba.