Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya bayyana cewa, ya tarar da jihar cikin wani mawuyancin hali a lokacin da ya karvi mulki.
Lawal, wanda ya bayyana hakan a yammacin Larabar da ta gabata a wani taron tattaunawa da ƙwararru a Jihar Zamfara a Abuja, ya ce, jihar na cikin wani hali kyau a lokacin da ya karvi mulki.
“Na yi imani da tarihin jiharmu, wannan shi ne karo na farko da ƙwararru da al’ummar jihar Zamfara ke zuwa don yin cuɗanya da juna.
“Na yi farin cikin jin wasu maganganun da aka yi. Lallai abin mamaki ne. Jihar Zamfara da muka gada tana cikin mummunan hali. A lokacin da muka karɓi mulki, Zamfara na cikin fara babu abin da ya rage.
“Jahar ce da muka gaji munanan abubuwa da yawa,” in ji shi yayin da yake amsa tambayoyi da tsokaci daga ƙwararru daga jihar.”
Gwamnan, ya ba da tabbacin cewa abubuwa za su canja da kyau. Lawal, ya ce, ya tarar da albashin wata uku ba tare da sisin da zai kula da ma’aikatan gwamnati ba.
Ya ce, duk da cewa jihar tana bin WAEC kimanin Naira biliyan 1.6 da NECO kimanin Naira biliyan 1.4 wanda hakan ya sa ɗaliban suka kasa cin jarabawar a baya, amma a baya-bayan nan gwamnatin sa ta biya NECO bashin.
Ya ƙara da cewa, gwamnatinsa ta fara aikin sake gina makarantun firamare tare da ƙara wa malaman kwarin gwiwa domin bunƙasa ayyukansu.
Ya ce, lokacin da ya shigo jihar Zamfara na da ma’aikatu 28 waɗanda a yanzu aka mayar da su ma’aikatu 16.
Gwamnan wanda ya koka da halin da asibitocin jihar ke ciki, ya ce ya jajirce wajen sauya duk wani yanayin. Don haka, ya nemi goyon bayan ƙwararru don gina jihar don amfanin jama’a.
Lawal ya ce, a ƙoƙarin da ake na tunkarar ƙalubalen tsaro a jihar, ya gana da babban hafsan tsaro, babban hafsan soji da kuma mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro a lokuta daban-daban.
Ya kuma ce ya gana da jami’an Tarayyar Turai da Bankin Duniya kan batutuwan da suka shafi rashin tsaro, ilimi, lafiya da kuma samar da ababen more rayuwa, kuma a shirye suke su ba da tallafi.