Gwamnoni da ciyamomi na wawushe kuɗaɗen da aka ware wa kansiloli – Buhari

Daga WAKILINMU

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi zargin cewa, gwamnoni da shugabannin ƙananan hukumomin ƙasar nan na sace kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya take ware wa kansiloli.

Wannan na zuwa ne kimanin sa’o’i 24 bayan da Ƙaramin Ministan Kuɗi, Mr. Clement Agba, ya zargi gwamnoni da jefa jihohinsu cikin talauci ta hanyar mayar da yankunan karkara saniyar ware a harkokinsu.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Laraba a Abuja, Agba ya ce gwamnonin sun maida hankali wajen gina filayen jirgin sama da gadojin sama a biranesu maimakon yi wa yankunan karkara hidima.

A nasa ɓangaren, Shugaba Buhari ya faɗa a ranar Alhamis cewa, gwamnoni da ciyamomi ne ke hana yankunan karkara bunƙasa yadda ya kamata ta hanyar wawushe kuɗaɗen da akan ware domin su.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen wani taro a Abuja.