Tun zamanin Jonathan rabon da NNPC ya sanya ko ƙwandala a asusun CBN – Emefiele

Daga AMINA YUSUF ALI

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya koka da yadda NNPC ya daina turo da Daloli kowanne wata ga asusun CBN ɗin. Wato wanda ya saba turowa na cinikin man fetur na ƙasashen waje zuwa ga CBN a kowanne wata.

A cewar Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, rabon da CBN ya ga wannan kuɗin na wata-wata da aka saba sakawa a asusunsa tun lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan. Wato tun daga shekarar 2014 kenan.

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN, Mista Godwin Emefiele ya bayyana takaicinsa a kan yadda kamfanin samar da man fetur ya daina zuba kuɗaɗen ne a taron laccar ma’aikatan banki da ƙungiyar ma’aikatan banki ta Nijeriya (CIBN) karo na 57 ta gabatar, wanda aka gudanar a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamban 2022 a jihar Legas.

Wannan a cewar sa, ya jawo kuɗaɗen da suke ajiye na ko-ta-kwana a Babban Bankin kullum ƙara raguwa suke da Dalar Amurka biliyan uku wato Naira tiriliyan uku da kusan rabi inda har sun koma yanzu ba ko ƙwandala, a cewar sa. Kuma a cewar sa wannan shi ya ƙara jefa ƙasar cikin jidalin ƙarancin kuɗaɗen canji. Kuma a sakamakon hakan darajar Naira take ƙara faɗuwa a cewar sa.

Hakazalika, Emefiele ya koka da yadda satar ɗanyen man fetur take ƙara ta’azzara kuma abinda yake daƙile yawan man fetur ɗin da Nijeriya take fitarwa don cinikinsa a ƙasashen wajenta.