An cafke tsoho mai shekara 70 bisa zargin yi wa ‘yar shekara 13 fyaɗe a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Kwamitin musamman kan yaƙi da bangar siyasa, shaye-shaye da sauran laifuka da Gwamnatin Zamfara ta kafa a jihar, ya kama wani tsoho mai shekara 70 nisa zargin yin lalata da wata yarinya ‘yar shekara 13 a Gusau, babban jihar.

Shugaban kwamitin, Hon. Bello Mohammed Bakyasuwa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai ranar Juma’a.

A cewarsa, wanda ake zargin ya amsa laifin yi wa yarinyar fyade har sau biyu, kuma jami’an kwamitin ne suka kama shi a lokacin da yake ƙoƙarin yi mata fyade a karo na uku a Unguwar ‘Yan mangwarori da ke Gusau a ranar Alhamis.

A wata hira da manema labarai, wanda ake zargin ya bayyana cewar yana da mata huɗu da ‘ya’ya 20.

Ya amsa cewa ya yi hulɗa da budurwar sau biyu a lokuta daban-daban a gidansa.

Wanda ake zargin dai shi me shugaban ƙungiyar NATO reshen Jihar Zamfara, ya musanta cewa ya ɓata yarinyar, tare da cewa mazakutarsa ba ta aiki.

“Ko likitoci sun tabbatar da cewa mazakutata ta mutu kuma na yi nadamar abin da na yi,” inji shi.

Ya ce, ya lallashi yarinyar ne ta hanyar ba ta kuɗi Naira 100 da Naira 200 sannan ya samu ya aikata wannan mummunan al’amari a karon farko da na biyu kafin daga bisani matansa su fallasa shi.

Iyalansa sun tona asirinsa ne ta hanyar sanar da kwamitin yaƙi da ‘yan bangar siyasa wanda hakan ya sa aka kama shi.

Kazalika, shugaban kwamitin ya ce, jami’ansa sun kama wani yaro mai matsakaitan shekaru bisa zargin fasa shaguna tare da satar babura da kuma wasu ‘yan mata biyu da mai agwagwa da buje ɗauke da miyagun ƙwayoyi a tsakar dare suna yawo a garin Gusau bisa zargin aikata wasu munanan ɗabi’u.

Ya ƙara da cewa, nan ba da jimawa ba kwamitinsa zai miƙa waɗanda ake zargin ga hukumomin da suka dace domin ɗaukar mataki na gaba.