Maƙudan kuɗaɗe duk tawagar da ke Gasar Kofin Duniya a Qatar za ta samu – Rahoto

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wani rahoton Sky Sports ya bayyna cewa, Hukumar Kula da Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) ta qara yawan kuɗin kyautar da ake bai wa ƙasashen da suka samu gurbin buga gasar kofin duniya da ke gudana a ƙasar Ƙatar, da dala miliyan 40 maimakon dala miliyan ɗari 400 da ake kashewa.

Tun a watan Afrilun wannan shekarar ne dai hukumar ta FIFA ta sanar da bai wa ƙasashen da suka samu gurbin buga gasar dala miliyan daya da rabi don shirya wa gasar.

Haka nan kowace tawagar ƙasar da ta halarci gasar ta bana cikin 32 sai da aka ba su dala miliyan 9 a matsalin kuɗin rukuni.

Duk wata ƙasa da ta samu damar tsallakawa zuwa zagaye na biyu na gasar, za ta samu dala miliyan 13, inda a jimillance ƙasashe 16 za su raba dala miliyan ɗari da huɗu.

Sai matakin zagayen daf da na kusa dana ƙarshe wato ‘quarter-finals’, inda qasashe 8 da suka kai wannan mataki za su samu dala miliyan 68, inda kowaccen su za ta samu dala miliyan 17.

Ƙasar da ta ƙare a mataki na huɗu za ta samu dala miliyan 25, sai kuma wacce ta kare a mataki na uku za ta samu dala miliyan 27.

Haka nan hukumar FIFA ta ware kyautar dala miliyan 30 ga duk ƙasar da ta kare a mataki na 2.

Duk ƙasar da ta samu nasarar lashe gasar ta bana kuwa zata samu zunzurutun kuɗi har dala miliyan 42.