Sojojin Nijeriya sun kashe mayaƙan ISWAP da ke ƙera boma-bomai a tafkin Chadi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu hare-hare ta sama da jiragen yaƙin rundunar sojojin saman Nijeriya NAF suka kai, sun kashe ‘yan ta’adda 24 na ƙungiyar Da’esh ta yammacin Afirka ISWAP.

Jaridar PRNigeria ta tattaro, ya faru ne a ranar Lahadi, a Tumbun Hamma, ɗaya daga cikin wuraren da aka gano sansanonin horar da ƙungiyar ISWAP a tafkin Chadi.

‘Yan ta’addan da aka kakkaɓe, kamar yadda wata majiyar leƙen asiri ta tsaro ta shaida wa PRNigeria, suna gudanar da aikin sarrafa makamai da IED, suna horo a wurin na tsawon kwanaki shida a jere.

A wani labarin makamancin haka, PRNigeria ta tattaro cewa wani jirgin sama na sojojin saman Nijeriya NAF ƙarƙashin rundunar sojojin sama na Operation Haɗin Kai, OPHK, sun kai wasu hare-hare ta sama a kan wuraren da ‘yan ta’addan ke Tumbun da ke kusa da tafkin Chadi.

Wannan wani ɓangare ne na harin ramuwar gayya ta sama da aka kai wa ‘yan ta’adda bayan yunqurinsu na kai hari a wani sansanin sojojin Nijeriya da ke Mallam Fatori.

A cewar wata majiyar soji, bayanan sirri sun nuna cewa ‘yan ta’adda na kutsawa cikin Mallam Fatori daga Tumbun Fulani, kuma suna ɗauke da manyan motocin bindiga guda 4, da makaman tallafi da dama, da sauran fasahohin zamani.

“Saboda haka buƙatar aikin hana zirga-zirgar jiragen sama don ragewa da daƙile ayyukansu. Saboda haka, harin da aka kai wa Fulanin Tumbun ya kai ga lalata 3 daga cikin manyan motocin bindigu da ke ɓoye a ƙarƙashin bishiya tare da ‘yan ta’adda da dama da suka fantsama zuwa kwale-kwale 6 a gabar tafkin Chadi su ma an kawar da su, wanda hakan ya ba ta ƙarfin da za su iya kai wa nasu farmaki,” inji sh.

Ƙoƙarin jin ta bakin Daraktan Yaɗa Labarai na Tsaro, Manjo Janar Jimmy Akpor, ko Kakakin NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, don jin ta bakinsa, ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.