Haƙar Ma’adanai: Gwamnatin Tinubu ta samu sama da Dala miliyan 800 na hannun-jari daga waje – Minista

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ɓangaren haƙar ma’adinai a Nijeriya ya samu gagarumar nasara, wanda Ministan Raya Ma’adinai, Dakta Dele Alake, ya bayyana a matsayin “ci-gaba mafi girma da aka taɓa samu a tarihin Najeriya” a fannin.

A cewar Ministan, kuɗaɗen shiga daga harkar ma’adinai sun ƙaru daga Naira biliyan 6 a baya zuwa biliyan N38 a shekarar 2024, hakan ya kai ninki shida cikin shekara guda.

Ci-gaban ya biyo bayan sabbin matakai ne da aka kafa, waɗanda suka haɗa da tsauraran sharuddan bayar da lasisi da kuma wajabcin sarrafa ma’adanai a cikin gida kafin a fitar da su zuwa ƙasashen waje.

Matakan sun janyo hannun-jari daga ƙasashen waje da ya kai fiye da Dala miliyan 800, inda manyan ƙasashen duniya suka fara nuna sha’awar saka jari a fannin ma’adanan da duniya ke matuƙar buƙata.

Daga cikin manyan ayyukan da Ma’aikatar Raya Ma’adanai ke aiwatarwa sun haɗa da; Masana’antar lithium mai darajar $600m a kan iyakar Jihohin Kaduna da Neja, Masana’antar tace ma’adanai mai darajar $200m a Abuja, wacce ke dab da kammaluwa, da kuma masana’antu biyu da za a gina a Jihar Nasarawa a zango na uku na shekarar 2025.

Duk da cewa an saki kashi 18% kacal daga cikin kasafin kuɗin ma’aikatar, wanda ya kai Naira biliyan 29, an samu nasarori masu girman gaske. A zangon farko na shekarar 2025, Hukumar Rijistar Ma’adanai (MCO) da Sashen Binciken Ma’adinai sun tara kuɗaɗe har Naira biliyan 6.9 da biliyan N7, wanda ya wuce yawan da ake samu a baya.

A wani mataki na tabbatar da daidaito, Ministan ya ce an kama sama da mutum 300 da ke haķar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, tare da kafa gamayyar haķar ma’adanai fiye da 250 domin ƙarfafa harkar.

Haka kuma, Nijeriya ta samu matsayin jagorantar Ƙungiyar Dabarar Ma’adanai ta Nahiyar Afirka (Africa’s Mineral Strategy Group).

Gwamnatin Tarayya kuma ta ƙaddamar da kasafin kuɗin Naira tiriliyan 1 wanda zai taimaka wajen janyo ƙarin jarin ƙasashen waje.

Al’umma da masana tattalin arziƙi sun bayyana matakin gwamnatin Tinubu a matsayin sauyi mai ma’ana da zai iya canza fasalin tattalin arziƙin Nijeriya gaba ɗaya, musamman a fannin da aka jima ana watsi da shi.

Wannan ci-gaban wata alama ce da ke nuna yadda shugabanci mai hangen nesa da tsare-tsaren da suka dace zai iya farfaɗo da sassan tattalin arziƙin ƙasa da ke da tasiri wajen samar da aikin yi, ƙara kuɗaɗen shiga da tabbatar da ci-gaban ƙasa mai ɗorewa.

By Babaji