Haɗin kan Sin da Argentina ya zamo abin misali ga ƙasashe masu tasowa

Daga CMG HAUSA

A bana ne ake cika shekaru 50 da kafuwa hulɗar diplomasiyya tsakanin Sin da Argentina.

A matsayin ɗaya daga cikin wasu ayyukan murnar wannan muhimmin lokaci, kana shekarar sada zumunta tsakanin ƙasashen biyu na shekarar 2022, an gabatar da dandalin manyan shugabanni, na mu’amalar al’adu tsakanin ƙasashen biyu, inda shugabannin ƙasashen biyu suka aikewa juna wasikar taya murna.

Abin da ya bayyana cewa, shugabannin ƙasashen biyu na dora babban muhimmanci kan haɗin kansu.

A cikin wadannan shekaru 50 da suka gabata, dangantakar dake tsakaninsu ta sauya, daga abokai masu nisa da juna zuwa abokan haɗin kai a dukkanin fannoni, matakin da ya amfani al’ummominsu, kuma ya shaida cewa, za a iya cimma moriya tare.

Mu’ammalar al’adu da cuɗanyar al’ummomin biyu, tushe ne na haɗin kan Sin da Argentina a cikin wadannan shekaru 50 da suka gabata.

Daga cikinsu kuma, haɗin kan kafofin yada labarai na ba da muhimmanci matuƙa.

A gun dandalin manyan shugabanni na mu’amalar a’adu, kafar CMG ta ƙasar Sin, ta sanar da haɗin kai da kafofin yada labarai na Argentina, don shirya “makon al’adun ƙasashen biyu”, da kafa “salon yada labaru da ɗumi-ɗumi tsakanin Sin da ƙasashen Latin Amurka” da dai sauransu.

Sakantare mai kula da kafofin yaɗa labarai na kasar Argentina Juan Ross ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, yana mai cewa, Sin da Argentina sahihan abokan haɗin gwiwa da aminai ne dake haifar da moriyar juna.

Mai fassara: Amina Xu