APC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu na tabbatar da Machina ɗan takarar sanata

Daga BASHIR ISAH

Jam’iyyar APC mai mulki ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke na tabbatar da Bashir Machina a matsayin ɗan takarar sanata a Yobe ta Arewa na APC a zaɓen baɗi.

Idan za a iya tunawa, a ranar 28 ga Satumba, 2022, wata Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Damaturu babban birnin jihar, ta tabbatar da Bashir Machina a matsayin wanda zai yi wa APC takarar sanata a shiyyar Yobe ta Arewa a 2023.

Kotun ta bai wa APC umarnin ta miƙa sunan Machina ga hukumar zaɓe INEC, a matsayin ɗan takara.

Dambarwar takarar sanata a Yobe ta Arewa ta fara ne bayan da Machina wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na APC, ya ce shi ba zai janye wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ba.

Tun farko, Sanata Lawan ya shiga takarar neman shugabancin ƙasa ne, inda ya gaza kai bantensa a zaɓen fidda gwanin da jam’iyyarsu ta shirya wanda hakan ya sa ya koma neman kujerar sanata.

Duk da dai babu wata shaidar cewa Lawan ya shiga zaɓen fidda gwani na sanata a shiyyarsu, sai dai Shugaban APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce da Lawan aka yi zaɓen fidda gwanin wanda hakan ya sa daga bisani aka ga sunan Lawan a jerin ‘yan takarar a maimakon sunan Bashir Machina wanda duniya ta shaida shi ne ya lashe zaɓen.

Duk da dai Lawan ya ce ya amince da hukuncin kotun, kwatsam, sai aka ji shugaban APC na jihar Yobe, Mohammed Gadaka ya ce jam’iyyar za ta ɗaukaka ƙara.