Zargin ɓatanci: Abduljabbar ya zargi lauyansa da karɓar cin-hanci na miliya N2

Daga BASHIR ISAH

Fitaccen malamin nan na Kano wanda ake zargi da ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW), Abduljabar Kabara, ya yi zargin lauyansa, Dalhatu Shehu-Usman ya karɓi kuɗi Naira miliyan N2 don bai wa alƙalin Kotun Shari’a ta Kano a ci gaba da shari’ar da ake yi masa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya rawaito ana tuhumar malamin ne da laifuka guda huɗu da suka haɗa da ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW) wanda ya aikata a ranakun 10 ga Agusta, 25 ga Oktoba da kuma 20 ga Disamba, 2019.

Yayin zaman da kotun ta yi a ranar Alhamis, lauyan mai kare kansa Shehu-Usman, bisa wakilcin Muhammad Lawan, ya buƙaci kotun da ta ƙyale Abduljabbar ya karɓi bayanansa na ƙarshe da ya rubuta da kansa.

A cikin bayanan nasa mai ɗauke da kwanan wata 20 ga Satumba, ya buƙaci kotun ta yi watsi da ƙarar da Gwamnatin Jihar Kano ta shigar a kansa sannan ta bai wa gwamnatin umarnin neman afuwarsa.

“Ina buƙatar kotu ta karɓi bayanaina a wannan shari’ar da kuma muryata ta wa’azin da na yi a matsayin hujja.

“Lauyana ya zo gidan yari ya faɗa mini cewa alƙali ya umarce shi ya karɓi Naira miliyan N2 don a sallame shi a kuma wanke shi.

“Lauyana ya faɗa mini cewa ya ba alƙalin miliyan N1.3, ya ba wani dubu N200,000, sannan shi ya ɗauki dubu N500,000,” inji shi.

Lauyan mai tuhuma, Mamman Lawan-Yusufari, SAN, ya buƙaci kotu ta yanke wa mai kare kansa hukunci daidai da doka, sannan ta riƙi bayanansu a matsayin hujja a kan mai kare kansa.