Ambaliya: An yi kira ga gwamnati ta kai wa manoma ɗauki

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An yi kira ga Gwamnatin Tarayya da na jihohi su kawo cikakken tallafi don agaza wa mutanen da ambaliyar ruwa ya shafa a ƙasar nan.

Dattijon Arewa, Alhaji Gambo Muhammad Ɗanpasa shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Kano.

Ya ce gonakin da ruwa ya lalata amfanin gonarsu a Jihar Kano kaɗai sun haura dubu shida, “wasu ma suna shirin girbi Allah ya kawo wannan ibtila’in, mutane da dama sakamakon haka sun shiga halin tagayyara, abinda za su ci da iyalansu ma babu. 

“Don haka ya kamata gwamnatoci su ɗauki mataki na gaggauta kawo musu ɗauki na tallafi don rage musu raɗaɗi, kuma a tabbatar abinda za a yi musu na taimako ya je ga waɗanda ya dace a basu domin ka da a yi sama da faɗi kamar yadda ya saba faruwa, don haka a ji tsoron Allah,” ya ce.

Alhaji Gambo Muhammad Ɗanpasa ya ƙara da cewa, “ba gwamnati kawai ba suma ‘yan kasuwa da duk wanda ke da hali ya kawo gudummuwa ga manoma da suka yi asarar amfanin gonarsu domin suna da matuƙar buƙatar taimako a wannan lokacin.”

Ɗanpass ya sake gargaɗin gwamnatoci a ƙasar nan a kan su tsahirta da  yawan karɓe-karɓen bashi da suke yi daga ƙasashen duniya, domin a cewarsa in ba a yi wasa ba za a wayi gari duk ma’adanan ƙasar nan zai koma hannun waɗanda aka karɓo basussuka a wajensu, su za su riqa juya komai.

Ya ce ba yanzu ake kallo ba, ana duba lokacin da za a ce a biya bashin babu abin biyan, hakan zai sa duk kadarorin ƙasar nan ya koma na masu bin bashin.

 Don haka ya ce Shugaban Ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki su haɗa ƙarfi da ƙarfe su ceci ƙasar nan, “in aka zura ido fa duk abinda ake ba a magana to ba a san yadda gobe za ta zo ba.”

Gambo Muhammad Ɗanpasa ya ce kusan da gangan aka ƙaƙaba talauci a ƙasar nan ta hanyar nakasta masana’antu, musamman masaƙu da ake da su a Kaduna da sauran jihohi da suke bada milki ga ɗimbin jama’a yanzu duk sun rasa ayyukansu ta yaya za a samu zaman lafiya babu aikin yi.