
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Saudiyya ta sanar da rage adadin mahajjatan da ta ware wa Nijeriya, wanda hakan ya tilasta wa hukumar jigilar alhazan Jihar Zamfara rage maniyyata guda 456 daga shiga sahun waɗanda za su je aikin hajji a 2026.
Shugaban hukumar, Musa Mallaha ya bayyana haka a wata hira da ‘yan jarida a Gusau, inda ya ce ragin ya sa aka zaftare wa Zamfara adadi daga 2,207 zuwa 1,741.
Saidai duk da haka, hukumar ta ce tana cigaba da shirye-shiryen aikin hajjin na bana, inda nan ba da jimawa ba gwamnatin jihar ta za fara jigilar maniyyata daga filin jiragen sama na Zamfara.
Mallaha ya kuma bayyana cewa, tuni aka ɗauki matakan da suka dace wajen inganta harkokin walwalar maniyyata ciki har da tallafin kayayyaki.
A cewarsa, kowane maniyyaci zai samu jakka mai girma guda biyu da ƙarama ɗaya, wanda ke nuna hakan ci-gaba ne daga na baya, inda ake samar wa maniyyaci jakka guda.
Ya ƙara da cewa, an kafa kwamiti da zai wayar da kan maniyyatan akan yadda za su gudanar da aikin hajjinsu bisa koyarwar fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW), wanda tuni ya fara aiki a ƙananan hukumomi 14 na faɗin jihar.
Har ila yau, shugaban hukumar ya jaddada aniyarsu ta cigaba da ƙoƙarin ganin an tabbatar da gudanar da aikin hajjin bisa tsari tare da kammalawa cikin lumana ga dukkan maniyyata.
