Hamayyar sarauta ta zama tarzoma yayin da magoya bayan Sanusi da Bayero suka yi artabu a fadar Sarkin Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rikici ya ɓarke a tsakanin magoya bayan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da na 16, Muhammadu Sanusi na 2, inda suak yi kiciɓis a Fadar sarki dake Ƙofar Kudu a Kano.

Lamarin ya auku ne lokacin da Sarki Aminu Ado ya nufi hanyar fadarsa ta Nasarawa daga gidansa na Mandawari.

Wani shaida ya ce, magoya bayan Bayero sun nufi hanayar fadar ne, inda Sarki Sanusi da muƙarrabansa suke bayan fitowa daga Mandawari, lamarin da ya haddasa rikicin da raunata masu gadi da dama da ƙone motocin ƴan sanda gami da fasa ƙofar fadar.

Rikicin shi ne wanda aka yi a kwanan nan tun bayan mayar da Sarki Sanusi kan karagar mulkin daga lokacin da aka yi wa kundin dokar masarautar garambawul a 2019, wanda ya kai ga raba ta gida biyar da kawo Sarki Aminu Ado kan kujerar sarautar Kano.

A sanarwar da tawagar yaɗa labarai ta masarautar ta fitar ta hannun kakakinta, Sadam Yakasai, ta zargi magoya Bayero da ƙoƙarin tada rikici da gan-gan, wanda hakan ya sa suka taho ta fadar da Sanusi ya ke a madadin bin hanyar zuwa Nasarawa.

Ta kuma zargi Sarki Bayero da ƙoƙarin amfani da hanyoyi masu fusatarwa domin nuna iko ga kujerar sarautar da nufin tsokanar magoya bayan Sanusi da al’umma baki ɗaya.

By Babaji