
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mazauna ƙauyuka da dama a Jihar Ondo sun shiga mawuyacin hali bayan da gidajensu da dukiyoyi suka lalace a sakamakon ambaliya da ta auku bayan samun mamakon ruwan sama na kwanaki uku.
Hanyoyi, gadaje da gidaje sun tarwatse, lamarin da ya ɗaiɗaita al’ummar yankunan da dakatar da harkokinsu na yau da kullum.
Wasu daga cikin ƙananan hukumomin da iftila’in ya shafa sun haɗa da Uso, Okitipupa, Ilaje, Ese-Odo da Akoko ta Kudu maso Yamma, lamarin da ya jefa masu ababen hawa cikin takura.
A Ƙaramar Hukumar Okitipupa, ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Ayeka, Ikoya, Igbodigo, Igodanlisa, Igbogunrin, Igbotako da kuma Ilutuntun.
Haka a yankunan ruwa na Ilaje inda ya shafi sansanin sojojin ruwa a Igbokoda a sakamakon haɗewar ruwan da ya haɗa yankunan Ilare, Omonira, Aboto, Ikuomola a garuruwan Mahin da Ugbo.
Mazauna yankunan sun kirayi gwamnatin jihar da hukumomin tarayya da su kawo musu ɗauki a yayin suka tsinci kawunansu a mawuyacin halin.
Babban sakatare daga ofishin mataimakin gwamnan jihar, Idowu Ojo, ya bayyana kaɗuwarsa game da faruwar iftila’in gami da alƙawaranta musu samun agajin gwamnati ga halin da suka samu kansu.
Ya kuma kiraye su da su ƙaurace wa zubar da shara a rafuka da magudanan ruwa, wanda hakan na taimaka wa afkuwar ambaliya.
