Kotu ta ayyana 17 ga Yuli a matsayin ranar hukunci kan buƙatar tafiya ta Yahaya Bello

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai Shari’a Maryann Anenih ta Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta ɗage sauraron saƙon takardar neman izinin yin tafiya da tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya shigar don zuwa neman magani a waje zuwa ranar 17 ga watan Yuli, 2025.

A yayin sake zaman sauraron ƙarar zargin badaƙalar kuɗaɗe da Hukumar EFCC ta shigar akan tsohon gwamnan ne, mai kare shi, Lauya Joseph Daudu (SAN) ya faɗa wa kotun cewa ya shigar da takardar neman tafiyar ne tun a ranakun 19 da 20 ga watan Yuni, 2025.

A ciki ne ya nemi kotun ta saki fasfo ɗin wanda ake tuhumar domin ya samu damar zuwa waje a duba lafiyarsa.

Saidai, a wata takarda daga ɓangaren EFCC, an ga yadda hukumar ta nuna rashin amincewa da buƙatar, inda ta ce bada damar hakan zai sa a samu jinkiri a yayin hukunci kan shari’ar.

Akan haka ne lauyan tsohon gwamnan ya ce sun sake shigar da wata takarda da ke neman a bada belin wanea ake tuhumar duba da cewa masu tuhumarsa sun shigar da ƙarar a kotuna mabanbanta.

By Babaji