
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shahararren babban ɗan kasuwa daga Jihar Kano kuma mai taimaka wa al’umma, Alhaji Amina Ɗantata ya rasu yana da shekaru 94 a duniya.
Wata majiya daga iyalan mamacin ta shaida wa jaridar ‘News Point Nigeria’ batun, inda ta ce ya rasu ne a wani asibiti dake Birnin Abu Dhabi a daren ranar Juma’a wayewar Asabar.
Marigayin ya rasu ne da misalin karfe 3 na dare agogon Nijeriya.
Ta kuma ce, an fara shirye-shiryen kawo gawarsa Nijeriya domin yin mata jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Sanannen attajirin, ɗaya ne daga cikin ƴan kasuwar da suka inganta harkokin kasuwanci acikin al’umma.
