Mutum uku sun mutu, bayan da suka faɗo daga bene a filin wasa a Algeriya, bayan busa tashi daga wasan da MC Alger ta lashe babban kofin lik na ƙasar, inji ministan lafiya.
Da dama kuma sun ji rauni a lokacin da shinge ya karye, bayan da ’yan kallo suka jingina don taya murna a filin wasa da ake kira 5 July Stadium a Algeria.
Sama da ’yan kallo 70 aka duba lafiyarsu a asibiti, kuma an sallami wasu da yawa daga cikinsu.
’Yan wasa da mahukuntan MC Alger sun je asibitin da aka kwantar da ’yan kallon, domin bayar da gudunmuwar jini ga masu buƙata ta gaggawa.
Filin wasan ya ɗinki da ’yan kallo a wasan da MC Alger ta kara lashe kofin da ta ɗauka a bara.
Tun kan a tashi daga karawar magoya baya suka kunna abubuwan tartsatsin wuta mai launin shuɗi da ya turnike filin.
Sakamakon haɗarin da ya faru ba a bai wa MC Alger kofin ba, sai nan gaba.
Tuni shugaban ƙasar Algeria, Abdelmadjid Tebboune ya mika ta’aziyyarsa ga waɗanda suka mutu, sannan ya yi fatan samun sauki ga waɗanda ke kwance a asibiti.
MC Alger ta samu ɗaukar kofin bana na biyu a jere, bayan tashi 0-0 da NC Magra.
