Dan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid Antonio Rudiger, ya shaida cewa ya fuskanci kalaman wariyar launin fata a wasansu da ƙungiyar Pachuca ta ƙasar Meɗico.
Antonio Rudiger dai ya zargi ɗan wasan baya na Pachuca, Gustavo Cabral wanda ɗan asalin ƙasar Argentina ne da furta masa kalaman wariyar, inda ya sanar da alƙalin wasan abun da ya faru.
Bayan an tashi daga wasan, mai horar da ’yan wasan na Real Xavi Alonso, ya kare ɗan wasan na sa.
“Ya shaida mana abun da ya faru, kuma mun yarda da kalaman na sa, kuma muna goyan bayansa. Za mu ga abun za a yi a kai.
Hukumar Kula da ƙwallon ƙafa ta Duniya FIFA na da dokoki na musamman da suka haramta irin wannan kalamai na wariya launin fata, a ciki da wajen filayen wasanni, don haka Xavi ya ce suna fatan za a yi bincike kan lamarin.
Idan har ta tabbata Gustavo ya yi waɗannan kalaman, za a ɗauki mataki mai tsauri a kansa domin ba abu ne da ba za a aminta da shi ba.
