Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kusan sojoji 20 aka kashe a wani hari amsa al’umma bindiga suka kai sansaninsu da ke kusa da Kwanan Dutse a ƙaramar Hukumar Mariga ta jihar Neja.
A cewar wata majiya daga jami’an da ke ƙaramar hukumar Shiroro da aka sanarwa faruwar lamarin sannan ta shaida wa Manhaja ta ce, ‘yan bindigar sun kai harin ne sansanin soji a ranar Talata da safe.
“An raunata wasu sojojin ma,” a cewar majiyar wacce ba a bai wa izinin magana da ‘yan jarida ba. Kuma majiyar ta tabbatar da an kai gawarwakin sojojin asibiti.
Har zuwa yanzu dai rundunar sojin Nijeriya ba ta ce komai ba kan lamarin ba. Kuma mai magana da yawun rundunar, Onyechi Anele, bai amsa kira da sakon neman ƙarin bayani da muka tura masa ba.
Kwamishinan tsaron cikin, Abdullahi Garba, shi ma bai amsa saƙon neman ƙarin bayani da muka tura masa ba.
Wannan hari na zuwa ne bayan awanni kadan da wasu ‘yan bindiga suka kashe mutane 15 mazauna ƙauyen Tofa da ke garin Magami ta ƙaramar hukumar Gusau a jihar Zamfara.
A dai wannan rana, an yi musayar wuta tsakanin yaran Bello Turji da jami’an tsaro waɗanda suka kashe kusan mutane 100 a kusa da ƙauyen Gida a ƙaramar hukumar Shinkafi a jihar Sakkwato.
Yawanci dai ‘yan bindiga a jihar Neja ba sa cewa su ne suka kai hari, amma wakilinmu ya fahimci cewa wurin da lamarin ya faru yana fama da kungiyar ‘yan bindiga ta Dogo Giɗe da wasu yaran marigayi Ali Kawaje.
Kamar sauran jihohin da ke fama da matsalar rashin tsaro, jihar Neja na fama da ƙungiyoyin ta’addanci dama ciki har da ta tsagin Boko Haram ta Sadiku.
Waɗannan ƙungiyoyin sukan kai hari ne kan fararen hula da jami’an tsaron masu haƙar ma’adanai. Sukan sace shanu da sace mutane domin neman kuɗin fansa da ɗin zarafin mata.
