Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Majidaɗi kuma Sakataren Masarautar Gumel, Alhaji Murtala Aliyu Muhammad, ya bayyana cewa babban abinda masarautar Gumel ƙarƙashin jagorancin mai martaba Sarkin Gumel Dakta Ahmad Muhammad Sani II sama da shekaru 45 na mulkinsa da kuma shekaru aru-aru da suka gabata na wannan masarauta ta Gumel babban abin da ta yi fice a kai shi ne zaman lafiya da karrama baƙo, kuma waɗanda suka zauna suka yi aiki anan su ne shaida a wannan magana domin kuwa da yawa saboda zaman lafiya da karrama baƙi da wannan masarauta ta yi suna in sun yi ritaya sukan zaɓi su zauna a Gumel domin cigaba da rayuwa, kuma wannan ya samo asali da bunƙasa ne sakamakon iya shugabanci na Sarkin Gumel ta yadda ke jan hankalin hakimai da sauran masu riƙe da sarautu da shugabanni na su karrama baƙo kada a yadda a yi wani abu na ba daidai ba da zai kawo tashin hankali kamar yadda ya ce.
Hakazalika ya ce ko da wani abu ne ya taso mai martaba Sarkin Gumel na ɗaukar matakai na masalaha domin warware dukkan wata matsala, kuma a cewarsa zai wahala a shekaru masu yawa da suka wuce ka ji wani abu na tashin hankali a wannan masarauta, inda ya ce wannan na da alaƙa na shugabanci na sauraron jama’a da addu’o’i da ake yi a kodayaushe a wannan masarauta ta Gumel wadda akwai buƙatar koyi da irin wannan shugabanci ga kowannemu.
Haka kuma wasu matakai da mai martaba Sarkin Gumel ke ɗauka a kodayaushe shi ne faɗakarwa da shugabannin gundunmomi, dagatai da masu unguwani shi ne kula da inda suke a ko da yaushe da kuma kawo rahoto da ake ga na da barazana da tsaro ko barazana da kiwon lafiya kamar faruwar wata cuta ko wata annoba da zarar an ganta domin ɗaukar matakin gaggawa.
Ya ce wannan na da daga cikin abubuwan da ke wanzar da zaman lafiya da cigaban wannan masarauta ta Gumel.
Haka abin yake a ɓangaren manoma da makiyaya ta hanyar faɗakar da su kula da haƙƙin maƙotaka ta hanyar kiyayye iyakar juna kamar kyakyawar zamantakewa a gidaje da wuraren noma da sana’o’i na yau da kullum ta yadda makiyayi zai guji shiga gonar manomi, kuma ya guji cinye burtali ko kawo wasu matsaloli a wajen shan ruwa dabbobi da makamantan su, wanda a kullum nasihar jagoran masarautar Gumel it ace iyaye a kula da tarbiyya yaya da kuma tura su makarantun addini dana zamani da sauran abubuwa masu amfani kamar zumunci da sauransu.
Majidaɗi a masarautar Gumel kuma sakatare Alhaji Murtala Aliyu Muhammad ya kuma yabawa kyakyawar alaƙa da ke akwai tsakanin masarautar da jihar Jigawa ta yadda ko a bukukuwan sallar babba da ta gabata sai da kwamishinoni biyu na filaye da na maadanai da kuma masu bawa gwamnan Jigawa Malam Umar Namadi ɗanmodi, shawara guda biyu da babban mai masauƙin baƙi a gidan gwamnatin jihar Jigawa domin taya sarkin Gumel murnar sallah lafiya.
Majidaɗi ya ƙarƙare da bayyana yadda masarautar Gumel ta gamsu da ayyukan bunƙasa noman rani da aka fara na gwaji a Galandi nan masarautar Gumel wanda gurin ya zama kamar kana kadawa ta Kano kuma gwamnan ya umarci a yi wannan tsari na bada hekta 100 a yi wannan noma a kowacce ƙaramar hukuma 27 da muke da su a Jigawa domin samawa matasa aikin yi da zai daƙile su daga zuwa cirani kudancin ƙasar nan bisa laaƙari da ake ciki yanzu da dai sauran ayyuka na gina asibitoci a wannan masarauta da sauran cigaban fannoni da wannan jiha ta samu daga gwamnatin jiha.
