Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wani mummunan al’amari ya faru a Abuja bayan da aka ruwaito cewa wani hamshaƙin attajiri mai suna Chief Godwin Chinedu Adimike ya rasa ransa bayan da ɗansa mai shekaru 21 ya kashe shi sakamakon wata zazzafar gardama da ta ɓarke tsakaninsu.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 15 ga Mayu, 2026, a gidan marigayin da ke lamba ta 3, titin Hassan Adamu, unguwar Guzape a Abuja.
Majiyoyi sun ce ana zargin ɗan nasa, wanda ke yi wa ƙasa hidima (NYSC), da caka wa mahaifinsa wuƙa sau da dama har ya mutu.
An ce rikicin ya fara ne bayan matashin ya nemi kuɗi daga mahaifinsa, inda yake zarginsa da rowa duk da tarin dukiyar da yake da ita. Rahotanni sun nuna cewa ya kwatanta kansa da abokansa waɗanda iyayensu ke saya musu motoci tare da ba su rayuwa mai armashi duk da cewa ba su kai mahaifinsa kuɗi ba.
A gefe guda kuma, marigayin ya zargi ɗansa da yin rayuwar almubazzaranci da kashe kuɗi ba tare da tsari ba.
Yayin da gardamar ta ƙara zafi, an ce matashin ya fusata tare da caka wa mahaifinsa wuƙa har sau uku, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa nan take.
Rahotanni sun kuma ce matashin ya dawo daga wani gidan rawa tare da wasu mata biyu kafin faruwar lamarin, kuma ana zargin suna wurin lokacin da rikicin ya auku.
A halin yanzu, ana tsare da wanda ake zargin a hannun jami’an ‘yan sanda yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan wannan mummunan al’amari.
