2027: Dan uwan TY ɗanjuma, Dinshiya, ya shiga takarar gwamnan Taraba

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Dan uwan tsohon Ministan Tsaro kuma dattijon ƙasa, Janar Theophilus Yakubu Danjuma (mai ritaya), Hon. Daɓid Usman Dinshiya, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Jihar Taraba a zaɓen 2027 ƙarƙashin jam’iyyar PDP mai biyayya ga Kabiru Tanimu Turaki.

Dinshiya ya bayyana hakan ne yayin wani taron jama’a da aka gudanar a Jalingo, inda ya ce burinsa shi ne dawo da fata tare da bunƙasa tattalin arzikin jihar Taraba.

Ya ce: “Taraba za ta iya yin fiye da haka. Taraba dole ta yi fiye da haka. Kuma tare, za mu gina Taraba mafi alheri.”

Ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, sarakuna, matasa, mata da magoya bayan jam’iyya a faɗin jihar.

Dinshiya ya nuna damuwa kan matsalar talauci, rashin aikin yi da kuma lalacewar ababen more rayuwa a jihar duk da yalwar albarkatun ƙasa da na ɗan Adam da Taraba ke da su.

Ya ce: “Matasa da dama ba su da aikin yi, manoma ba sa samun tallafin da suke buƙata, sannan hanyoyi da dama sun lalace kuma ba sa amfani.”

Ya yi alƙawarin cewa idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan noma, gina hanyoyi, kiwon lafiya, ilimi da samar da ayyukan yi.

A cewarsa, noma zai kasance babban ginshiƙi a gwamnatinsa saboda muhimmancinsa ga tattalin arzikin jihar.

“Za mu sauya noma daga na dogaro da kai zuwa hanyar samar da arziki ta hanyar amfani da injuna, samar da kayan aiki, wuraren ajiya da tallafin kuɗi ga manoma,” in ji shi.

Haka kuma, Dinshiya ya yi alƙawarin inganta harkokin lafiya da gina hanyoyi a sassan jihar.

“Za mu fara babban aikin gina hanyoyi domin haɗa al’ummomin jihar da hanyoyi masu inganci,” ya ƙara da cewa.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Taraba da su mara wa yunƙurin haɗin kai, ci gaba da walwala baya.

“Wannan zaɓe ba wai kawai zaɓen gwamna ba ne, zaɓen makomar Taraba ne,” in ji shi.

Dinshiya ya taɓa zama shugaban farko na Kwamitin Shugaban ƙasa kan Ci gaban Arewa maso Gabas da kuma babban jami’in farko na Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas (NEDC).

By ukarofi

Leave a Reply