Sojojin sama sun kashe gomman ‘yan bindiga a Neja

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Rundunar sojin sama ta Nijeriya ta ce ta kashe ‘yanbindiga da dama tare da daƙile harin da mayaƙan suka shirya a wani jerin samame da ta kai jihar Neja tsakanin 20 da 23 ga Mayu.

Mai magana da yawun rundunar Ehimen Ejodame ya ce an kai hare-haren ne a sassan ƙananan hukumomin Rafi da Mariga da ke jihar Neja.

Ya ce “a ranar 20 ga Mayu, sojojin sama sun farwa wani taron ‘yanbindiga a Tungan Bako da Kasuwan Daji a ƙaramar hukumar Rafi inda suka kashe ‘yan ta’adda da dama tare da tarwatsa mahaɗarsu.”

A ranar 21 ga Mayu ne rundunar sojin saman Nijeriya ta kai hare-hare kan ‘yanbindiga a Tungunguna zuwa Uregi da ke ƙaramar hukumar Rafi.

Sojojin saman kuma daga baya sun taimaka wa sojoji wajen daƙile ‘yanbindiga tare da ƙwace iko da yankin Tungan Makeri da ke ƙaramar hukumar Borgu.

Rundunar sojin saman a watannin baya-bayan nan ta tsananta kai samame kan ƙungiyoyin mayaƙa, lamarin da a wani lokacin ke shafar farar hula.

An zargi sojoji ma a farkon watan da muke ciki da kashe farar hula 12 a wani hari da suka kai kan Neja sai dai sun musanta lamarin inda suka ce hare-haren sun halaka fiye da ‘yanbindiga 70.

Neja dai tana fama da matsalar tsaro sakamakon ayyukan miyagu da ‘ynbindiga har ma da rikici tsakanin manoma da makiyaya.

By ukarofi

Leave a Reply