Za a iya warware matsalolin Nijeriya – Sarki Sanusi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa za a iya shawo kan matsalolin tsaro da tattalin arziƙin da ake fuskanta a ƙasar.

Ya ce ya kamata shugabanni da ’yan ƙasar su haɗa kai domin samun mafita mai ɗorewa.

Ya bayyana hakan ne a yayin bikin hawan sallah da aka gudanar a Kano, a ranar Laraba.

Sanusi II, ya ce Nijeriya na fuskantar manyan ƙalubale a fannin tsaro, tattalin arziƙi, da haɗin kai tsakanin al’umma, amma ya nuna ƙwarin gwiwa cewa za a iya samun mafita idan shugabanni suka yi adalci, sannan jama’a suka ba su goyon baya.

Ya yi wannan jawabi ne bayan ya jagoranci sallar Idi a filin Idi da ke Kofar Mata.

Ya kuma tunatar da Musulmi muhimmancin yin layya, yana mai cewa ibada ce da ke kusantar da bawa ga Allah.

Haka kuma ya ƙarfafi mutane da su taimaki marasa galihu.

Gwamna Abba Kabir Yusuf, mataimakinsa Murtala Sule Garo, da wasu manyan jami’an gwamnati sun halarci sallar.

Sarkin, ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da su koma ga Allah ta hanyar yin ayyukan da Ya yarda da su tare da guje wa abubuwan da ke jawo fushinsa.

Ya ce sauyi na gaskiya zai yiwu ne kawai idan mutane sun canza halayensu, yana mai jaddada muhimmancin ilimi, bin doka da oda, da kyakkyawar tarbiyyar yara.

Haka kuma ya roki ’yan Nijeriya da su ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro wajen yaƙi da rashin tsaro.

Tun da farko, Sanusi ya hau doki daga fadar Sarki zuwa filin Idi sannan ya koma fadar a matsayin wani ɓangare na bikin hawan sallah, wanda ya ja hankalin ɗimbin jama’a.

A wannan shekara, an fara gudanar da manyan bukukuwan hawa, bayan an dakatar da su na tsawon shekaru biyu sakamakon rikicin masarautar Kano.

By ukarofi

Leave a Reply