Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation HAɗIN KAI (OPHK) da ke aiki a yankin Arewa maso Gabas ƙarƙashin Operation DESERT SANITY ɓ/SIEGE OPERATIONS sun ci gaba da ƙarfafa nasarorin tsaro a yankin tare da tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da Sallar Eid El-Adha, yayin da suke ci gaba da matsa lamba kan ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka.
A wata babbar alama ta inganta tsaro da ƙarin amincewar jama’a, dakarun OPHK da ke yankin Ngoshe sun samar da cikakken tsaro tare da halartar Sallar Eid El-Adha tare da ‘yan sa-kai da mazauna yankin a Babban Masallacin Ngoshe cikin lumana.
Wannan mataki na da matuƙar muhimmanci kasancewar yankin a baya yana fuskantar barazanar hare-haren ‘yan ta’adda, lamarin da ke nuna tasirin ci gaba da hare-haren soji da dawo da zaman lafiya a hankali. Haka kuma, matakin ya yi daidai da ƙoƙarin dawo da ‘yan gudun hijira zuwa garuruwansu na asali cikin aminci.
A yayin addu’o’in da aka gudanar, an yi addu’a ga Rundunar Sojin Nijeriya, zaman lafiya a Arewa maso Gabas da kuma ƙasa baki ɗaya.
Haka zalika, dakarun Hedikwatar 26 Task Force Brigade ƙarƙashin OPHK sun samar da cikakken tsaro yayin Sallar Idi a masallatan da aka ware a garin Gwoza, lamarin da ya ba masu ibada damar gudanar da sallarsu cikin kwanciyar hankali da tsaro.
An kuma isar da saƙonnin fatan alheri daga manyan hafsoshin soja zuwa ga dakarun, domin ƙara musu ƙwarin gwiwa da jajircewa wajen ci gaba da ayyukan da suke gudanarwa.
A wani samame na daban, dakarun OPHK sun yi nasarar dakile wata barazanar fashi a ƙauyen Gar Gwigwi da ke ƙaramar hukumar Biu a jihar Borno bayan samun sahihan bayanan sirri.
A yayin samamen, an kama wasu da ake zargi da aikata laifuka guda uku da suka haɗa da Aliyu Mamadu, Umar Mohammed da Adamu Aliyu, waɗanda ake zargin suna addabar mazauna yankin. An cafke su ba tare da wata turjiya ba bayan waɗanda abin ya shafa sun tabbatar da su.
Kayan da aka ƙwato daga hannunsu sun haɗa da wayoyin hannu, agogon hannu, laya, wuƙa, kuɗi da kuma bindigar dane gun.
Binciken farko ya nuna cewa bindigar mallakin Mallam Manu Ibrahim ce, wani ɗan ƙungiyar Miyetti Allah da aka yi wa fashi kwana guda kafin samamen. Tuni aka mayar masa da bindigarsa domin nuna jajircewar rundunar wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
A wani ci gaban makamancin haka, dakarun OPHK tare da haɗin gwiwar Ciɓilian Joint Task Force (CJTF) sun kama wani da ake zargi da taimaka wa ‘yan ta’adda mai suna Alhaji Gambo mai shekaru 33 yayin binciken tsaro a lokacin da yake ƙoƙarin shiga garin Monguno.
Kayan da aka samu a hannunsa sun haɗa da kayayyakin gyaran mota da wasu kayayyakin amfani na yau da kullum. A halin yanzu yana hannun jami’an tsaro domin ci gaba da bincike.
Rundunar ta bayyana cewa duk da cewa yanayin tsaro a yankin na ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali, har yanzu akwai buƙatar taka-tsantsan saboda yanayin na iya sauyawa a kowane lokaci.
Sai dai rundunar ta tabbatar da cewa dakarunta na da ƙwarin gwiwa da jajircewa wajen kare al’umma tare da ci gaba da nuna ƙwarewa da nagarta a ayyukansu.
Operation HAɗIN KAI ta jaddada aniyarta na ci gaba da hana ‘yan ta’adda samun damar gudanar da ayyukansu tare da kare fararen hula da tabbatar da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Arewa maso Gabas.
Babban Hafsan Rundunar Sojin Nijeriya ya yaba da bajintar dakarun tare da ƙarfafa musu gwiwa su ci gaba da mamaye filin daga domin hana ‘yan ta’adda samun wata dama a yankin ayyukan Operation HAɗIN KAI.
