An zargi jami’an kurkukun Kuje da sace wa fursuna miliyan N120 lokacin bincike

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon shugaban bankin Skye Bank Plc, Tunde Ayeni, ya rasa zoben aurensa da kuma agogon hannu mai tsada da aka ce kudinsu ya haura naira miliyan 120 yayin wani samame da aka kai gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja.

A cewar kafar sadarwar SaharaReporters, wasu majiyoyi daga cikin gidan yarin sun yi zargin cewa wasu manyan jami’an Hukumar Gyaran Hali ta Nijeriya ne suka kwace kayayyakin yayin abin da aka bayyana a matsayin bincike a cikin gidan yarin.

Rahoton ya kuma ce tsohon mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da aka dakatar, Abba Kyari, wanda shi ma ke tsare a gidan yarin, ya rasa kimanin naira miliyan biyu a lokacin samamen.

Majiyoyi sun ce jami’an da suka gudanar da aikin sun hada da mataimakin babban jami’in kula da ayyuka na hukumar tare da wasu jami’an gidan yarin Kuje.

An kuma ce jami’an sun shiga harabar gidan yarin tare da karnukan DSS da kuma rigunan kariya daga harsashi, lamarin da ya jawo firgici tsakanin fursunonin.

Wata majiya ta ce an binciki Ayeni yayin samamen sannan aka kwace masa zoben aurensa da agogon hannu mai tsada.

“Daya daga cikin tsofaffin shugabannin Skye Bank da ke gidan yarin Kuje an bincike shi tare da kwace masa zoben aure da agogon hannu da kudinsu ya haura naira miliyan 120,” in ji majiyar.

Majiyar ta kuma yi zargin cewa Abba Kyari ya rasa kudinsa kimanin naira miliyan biyu a hannun jami’an da suka gudanar da samamen.

Rahotanni sun ce lamarin ya haddasa tashin hankali a gidan yarin, inda wasu fursunoni suka zargi jami’an da cin zarafi da amfani da iko ba bisa ka’ida ba.

Wata majiya ta bayyana cewa Ayeni na shirin shigar da korafi a hukumance kan jami’an da ake zargi da hannu a lamarin.

“Tsohon shugaban bankin na son shigar da kara a yanzu haka,” in ji majiyar.

An ce lamarin ya faru ne yayin wani bincike a cikin gidan yarin, amma wasu majiyoyi sun yi zargin cewa an kwace kudi da kayayyakin wasu manyan fursunoni ba tare da cikakken bayani ko rubuce-rubuce ba.

Sai dai ba a tabbatar da zarge-zargen daga wata majiya mai zaman kanta ba zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Gidan gyaran hali na Kuje ya dade yana jawo cece-kuce kan matsalolin tsaro, ciki har da hare-haren fasa gidan yari da kuma zarge-zargen nuna fifiko ko cin zarafi ga manyan fursunoni.

Tunde Ayeni, wanda tsohon shugaban Skye Bank ne kuma fitaccen ɗan kasuwa, na fuskantar shari’a kan zargin damfara ta kimanin naira biliyan 15.7.

A baya-bayan nan wata babbar kotun Abuja ta ba shi beli na naira miliyan 200 tare da sharudda masu tsauri, ciki har da gabatar da masu tsaya masa da kuma garantin banki na naira biliyan 15.

Shi kuma Abba Kyari na fuskantar shari’a kan zargin safarar miyagun kwayoyi da sauran laifuka.

Zuware lokacin hada wannan rahoto, Hukumar Gyaran Hali ta Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan zarge-zargen ba.

By ukarofi

Leave a Reply