Dalilin da ya sa tsohon Minista Uche Nnaji ke son zama gwamnan Enugu – Rahoto

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Wani rahoto na musamman da jaridar Premium Times ta wallafa ya bayyana cewa tsohon Ministan Kirkire-kirkire, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, na matuƙar son zama gwamnan Jihar Enugu a zaɓen 2027 saboda zargin jabun takardun karatu da ake bincikensa a kai.

Rahoton ya ce duk da binciken da Hukumar ICPC ke yi kan zargin jabun digiri da takardar bautar ƙasa (NYSC), Nnaji ya fito takarar gwamna a karkashin wani ɓangaren jam’iyyar PDP mai alaƙa da Ministan Abuja, Nyesom Wike.

A watan Oktoban 2025 ne Premium Times ta wallafa wani bincike da ya ɗauki tsawon shekaru biyu, inda aka zargi Nnaji da gabatar da jabun takardun digiri da NYSC ga Shugaba Bola Tinubu da Majalisar Dattawa yayin tantance shi a matsayin minista.

Kwana uku bayan wallafa rahoton ne Nnaji ya yi murabus daga mukaminsa na minista.

Daga baya ya fice daga APC zuwa PDP bayan ya kasa lashe zaɓen gwamna a Enugu a 2023.

A watan Fabrairu na wannan shekarar ne aka rahoto cewa ICPC ta fara bincike kan zargin jabun takardun da ake yi masa, kuma akwai yiwuwar gurfanar da shi a kotu idan aka tabbatar da laifin.

Har ila yau, a watan Maris, wani kwamitin bincike da Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya kafa ya gano cewa Nnaji ya yi amfani da jabun takardun digiri da NYSC.

Majiyoyi daga Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha, Ma’aikatar Ilimi da kuma wasu na kusa da Nnaji sun shaida wa Premium Times cewa tsohon ministan na neman zama gwamna ne domin samun kariyar doka daga yiwuwar gurfanar da shi.

Rahoton ya ce Nnaji na fargabar cewa idan aka same shi da laifi, zai iya fuskantar hukunci da kuma rasa damar riƙe mukamin gwamnati nan gaba.

Kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 ya bai wa shugaba, mataimakinsa, gwamnoni da mataimakan gwamnoni kariya daga gurfanarwa a kotu yayin da suke kan mulki.

Wata majiya ta ce: “Yana ganin makomarsa na cikin rashin tabbas saboda wannan zargin jabun takardu. Saboda haka yana tunanin idan ya zama gwamna, aƙalla ba za a gurfanar da shi ba na tsawon wa’adin mulkinsa.”

Majiyar ta ƙara da cewa Nnaji na ganin idan ya samu wa’adi biyu, zuwa lokacin yawancin mutanen da ke bincikensa za su bar mulki.

Rahoton ya kuma ce Nnaji na fargabar gwamnatin tarayya za ta iya miƙa sakamakon binciken Ma’aikatar Ilimi ga Daraktan Gurfanar da Masu Laifi domin a tuhume shi.

Haka kuma, akwai rahotannin cewa Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Enugu na duba yiwuwar neman izinin gurfanar da shi saboda zargin ya shafi Jami’ar Nijeriya da ke Nsukka (UNN), wacce ke cikin jihar.

Rahoton ya kawo misalan wasu ‘yan siyasa da suka tsallake matsin lambar bincike bayan sun samu mukaman da ke ba su kariyar doka.

Daga ciki akwai gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, wanda EFCC ta bincika bayan ya bar kujerar Ministan Abuja, amma binciken ya tsaya bayan ya zama gwamna a 2019.

Haka kuma tsohon gwamnan Abia, Theodore Orji, ya lashe zaɓen gwamna a 2007 yana tsare a hannun EFCC, kafin daga bisani a sake shi bayan samun kariyar kundin tsarin mulki.

By ukarofi

Leave a Reply