
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jinjina wa marigayiya Alhaja Abibatu Mogaji, wato mahaifiyar Shugaba Bola Tinubu, inda ya bayyana ta a matsayin wadda soyayyarta ta kere ga iyalanta kaɗai ta amfani hatta Nijeriya a matsayinta na ƙasa.
A cewarsa, jagorancin marigayiyar, wadda ta rasu a shekarar 2013 tana da shekaru 96 a duniya, ya yi tasiri acikin al’umma ta yadda ya wuce iya furucin baka yak ai ga gani a ƙasa.
Da yake jawabi a babban taron addu’ar ƙasa da aka yi a Abuja domin karrama Alhaja Magaji a Babban Masallacin Ƙasa, Sanata Shettima ya ce ta yi wa al’umma hidimar da za jima ana mora a matakin jiharta Legas da ma ƙasa baki ɗaya har illa ma sha Allah.
Musamman a wata sanarwa da Kakakinsa, Stanley Nkwocha ya fitar, Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana tasirin da tarbiyyarta ta yi akan Shugaba Tinubu wajen horar da shi akan gogewar rayuwa da zama jagora, lamarin da a cewarsa ke cigaba da wanzuwa a Nijeriya ta shugabancinsa.
Ya bayyana cewa, marigayiyar ta kasance mai nagarta a fannin kasuwanci musamman akan ɗaukarsa a matsayin ginshiƙin hidimta wa jama’a da kuma mayar da shi fagen haɗuwa akan buƙatu da kare mutunci.
Ya kuma tunatar da yadda ta yi amfani da sama da rabin rayuwarta wajen kula da walwalar ƙananan ‘yan kasuwa wajen muhimmanci gina zamantakewarsu kaɗan da kaɗan saboda jarumtarta.
A ƙarshe, ya yi hajiyar addu’ar samun rahamar Allah a gare ta da kuma roƙon cigaba da wanzuwar alkhairan da ta shuka a bayan ƙasa acikin al’ummar Nijeriya.



