Kano: An samu jinkirin kayan zaɓe a rumfar zaɓen ƙofar gidan mai unguwa ta mazaɓar Dakata

Daga AMINA YUSUF ALI

A halin yanzu dai shaɗayan rana ta wuce ana cigaba da dakon kayan aikin zave daga INEC don fara gudanar da zaɓe a mazaɓar dakata ta jihar Kano.

Inda abin yake faruwa kuwa shi ne, akwatin da yake ƙofar gidan mai unguwa na wannan yanki na mazaɓar dakata.

A halin yanzu dai al’umma sun yi dafifi sun fito domin kaɗa ƙuri’unsu a wannan rumfar zaɓe mai akwati tara, amma shiru kake ji kamar an shuka dusa.

Wani shaidar gani da ido mai suna Malam Jibril wanda shi ma ɗan mazaɓar ta dakata ne ya bayyana cewa, yawancin ma rumfunan zaɓen da suke a yankin na Dakata har yanzu ba su samu kayan zaɓe ba.

Ya ƙara da cewa a kwai rumfar zaɓe ma ta Ofishin WAEC mai akwatunan zaɓe 5 da wasu da dama su ma har yanzu shiru kake ji.

Daga ƙarshe, Malam Jibril Auliya ya roƙi hukumar ta INEC ta duba lamarin ta kawo musu ɗauki.