Zaɓen 2023: Buhari ya kaɗa ƙuri’arsa

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari tare da mai ɗakinsa, Aisha, gami da sauran ahalinsa sun kaɗa ƙuri’arsu a rumfar zaɓe ta 003, a Sarkin Yara A, Ƙofar Baru da ke Daura, Jihar Katsina.

Bayanai sun nuna Shugaba Buhari da ahalin nasa sun isa rumfar zaɓen ne da misalin ƙarfe 9.57 na safe.

Ba da ɓata lokaci ba aka tantance Buhari kana aka ba shi damar kaɗa ƙuri’arsa.

Buhari ya yi kira da a yi zaɓe cikin lumana kana ‘yan takara kowa ya yarda da sakamakon zaɓen bayan kammalawa.