Da ɗumi-ɗumi: INEC ta ɗage zaɓen kujerar Sanatan Enugu ta gabas

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, (INEC), ta sanar da ɗage zaɓen kujerar Sanata na Enugu ta gabas zuwa 11 ga watan Maris na wannan shekarar. Hakan ya biyo bayan kisan ɗan takarar wannan kujerar na jamiyyar LP, Barista Oyibo Chukwu, wanda aka yi a ranar Laraba, 22 ga Fabrairun 2023.

Shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a yayin taron ‘yan jarida ɗazu a Abuja.

A cewar sa, wannan sanarwa ta dogara ne da dokar zaɓe ta kundin mulkin ƙasar nan da ta ba wa jamiyyar da ta rasa ɗan takararta dama ta kwananki 14 don samo wani wanda zai maye gurbin wanda ya mutu.

Daga ƙarshe shugaban na INEC ya bayyana cewa, zaɓen Sanatan na Enugu ta tsakiya da aka ɗage, za a yi shi ne tare da sauran zaɓuɓɓukan gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi.