Harin ISWAP a Maiduguri ya yi sanadiyar jin raunin yarinya ‘yar watanni

Daga AISHA ASAS

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Barno ta tabbatar da jin raunin yarinya ‘yar watanni shida da haihuwa a sanadiyar harin da ƙungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP ta kai a Maiduguri ta hanyar jefo bama-bamai har biyar.

Kwamishinan ‘yan sanda Abdul Umar, ya sheda wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN cewar, maharan sun harbo bama-bamai ne daga wajen filin jirgin sama na Ngomari, wanda ke bayan jami’ar Barno.

Ya ƙara da cewa, harin na su ya sauka a wurare ma-banbanta, hakan ne ya sa ba a samu hasarar rayuka ko kuma manyan raunuka ba.

Kwamishinan ya ce, bam na farko ya faɗa a gidan wani mutum da ake kira Ibrahim Abba-Fori, yayin da ya ƙona mota ƙirar Honda Civic.
Hakazalika ɗaya daga cikin bama-baman ya ruguza ɗakin wani bawan Allah mai suna Alhaji Bukar Modu-Kullima, tare kuma da zama sanadin jin raunin yarinya ‘yar kimanin watanni shida mai suna Fatima Alhaji-Bukar.

“Wani daga cikin harin ya sauka ne a gundumar Gambari Njimtilo, kusa da gidan Ahmed Yahaya, wanda ya yi sanadiyar rushewar katangar gidansa.” Cewar Abdul

Ya ƙara da cewa, “na ƙarshe a bama-baman ya sauka ne a wata gona da ke ƙauyen Shuwarin Atom.”

Kwamishinan ya tabbatar da cewa, babu rayuwar da ta salwanta a wannan harin. Kuma an baza ‘yan sanda da sojoji a muhallin da aka kitsa wannan harin. Ya kuma ƙara da ba da tabbacin hukuma za ta yi iya ƙoƙarinta don ganin hakan ba ta sake aukuwa ba.

Game da yarinyar da ta ji rauni kuwa, Umar ya bayyana cewa, an kaita asibitin Umaru Shehu Ultra Modern Hospital, inda aka ba ta magani, kana aka sallame ta duba da cewa raunukan na ta kaɗan ne, don haka ba sa buƙatar kwanciya. Ya kuma ƙara da kira ga al’umma mazauna wannan yanki, da su buɗe ido tare da hanzarta kai rahoton duk wani abu da ka iya taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci.

Daga ƙarshe ya kwantar da hankalin mutane, tare da ba su tabbacin hukuma za ta yi iya kokari wurin kare rayukansu da kuma dukiyoyinsu.