Harin Sakkwato: A kan idona mahaifiyata da ‘ya’yana 5 suka ƙone ƙurmus – Shafa’atu

Daga BASHIR ISAH

Ɗaya daga cikin matafiyan da harin Sakkwato ya rutsa da su mai suna Shafa’atu, ‘yar shekara 30, ita ce mutum ɗaya tilo da ta tsirar daga mummunan harin da ya laƙume gomman matafiya.

Shafa’atu ta labarta yadda ‘ya’yanta biyar suka ƙone ƙurmus a kan idonta ciki har da jaririya ‘yar wata goma da haihuwa.

Haka nan, ta ce ta rasa mahaifiyarta da wasu ‘ya’yan ‘yan’uwa a harin da ya auku ranar Litinin da ta gabata a ƙauyen Gidan Bawa a hanyar Sabon Birni.

Da take bayani daga inda take jinya alhalin duka jikinta ƙunar wuta ne, matar ta ce fasinjoji sama da 40 ne harin ya rutsa da su a cikin bas ɗin.

Ta ce, “Akwai dattawa su 33 a cikin motar da yara ƙanana da dama, amma mutum biyu ne kawai suka tsira da ransu bayan da motar ta kama da wuta sakamakon harbin bindigar ‘yan ta’addan.

“Daga bisani ɗaya fasinjan da ya tsira ya rasu a asibiti sakamakon raunin da aka yi masa da alburushi.

“Gaskiya ba abu ba ne mai sauƙi ka ga yadda mahaifiyarka da ‘ya’yanka da sauran ‘yan’uwa suke ihu saboda ƙunar wuta har su ƙone ƙurmus a gabanka.”

Shafa’atu wadda a halin yanzu take ci gaba da samun kulawa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ɗanfodiyo a Sakkwato ta ce, a wannan rana suna hanyarsu ta zuwa Kaduna ne kafin daga bisani maharan suka rutsa su.