
Daga BELLO A. BABAJI
An tsare wasu sojoji biyu da aka alakanta su da Bataliya ta 135 ta jami’ai na musamman bisa zargin su da hada kai da ƴan ta’addar ISWAP wajen tada zaune-tsaye ga zaman lafiya a Jihar Yobe.
Jami’an tsaron da ke aiki a bangaren sadarwa sun bi diddigin tattaunawar da sojojin suka yi da ke da alaka da garkuwa da matafiya a ranar 9 ga watan Mayu, 2025 a hanyar Gashua zuwa Azare a jihar.
Wani shaida da ke da kusanci da batun ya ce, sojoji biyun sun tsegumta wa mayakan ISWAP tsarin sintirin sojoji a yankin Burata, Kamuya, Azare da Gashua.
Lamarin da ya bai wa mayakan damar kai farmaki a babbar hanyar yankin, kana daga bisani dakarun tsaro suka dakile shi tare da tarwatsa mayakan.
Haka ma kwararre akan sharhi game da hanyoyin magance ayyukan tada kayar baya a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce butulcin an yi shi ne da nufin bai wa ƴan ta’addar damar kai farmakin, wanda daga bisani sojoji suka mayar da martani tare da ceto wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su da wasu makamai.
Ya kuma ce, tun daga nan ne sojoji suka fara bincike kan lamarin, inda a yanzu biyun da aka tsare ana gudanar da bincike akan su, saidai ba a bayyana sunayensu ba saboda wasu dalilai.
