Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wasu mutum bakwai sun rasa ransu sakamakon hatsarin kwale-kwale lokacin da suke tafiya daga ƙauyen Gidan Husaini zuwa Gwargawu na ƙaramar hukumar Shagari a jihar Sakkwato ranar Litinin.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da mamatan ke tafiya a wani kogi, lamarin da ya jefa mutanen yankin cikin jimami da alhini.
Ba a dai bayyana sunayen waɗanda suka rasun ba, amma hukumomi a yankin sun tabbatar da cewa dukkan mamatan ’yan asalin ƙauyen na Gidan Husaini ne.
Da ya jagoranci wata tawagar gwamnatin jihar domin yin ta’aziyyar mamatan, Kwamishinan Kuɗi na jihar, Muhammadu Jabbi Shagari, ya bayyana hatsarin a matsayin rashi ga ilahirin mazauna yankin, jihar da ma al’ummar Musulmi bakiɗaya.
Sai dai Kwamishinan ya yi kakkausan gargaɗi ga matuƙa kwale-kwalen a kan yin lodin da ya wuce kima, inda ya ce rayuwar mutane ta fi komai za a samu muhimmanci.
Sai dai hatsarin ya sake fito da damuwar da ake da ita kan harkar sufuri ta ruwa a yankunan karkarar jihar, inda mutane suka dogara da kwale-kwalen saboda ƙarancin jiragen ruwa.
