Hatsarin kwale-kwale ya yi sanadin mutuwar mutum 40 a Kano

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Aƙalla mutane 40 wanda akasari mata da yara ne aka ruwaito sun rasa rayukansu a qauyen Badau da ke qaramar hukumar Bagwai a jihar Kano sakamakon wani hatsarin kwale-kwale.

Wani wanda abun ya faru a gaban idonsa wanda kuma ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce, hatsarin ya faru ne a ranar Talata da misalin ƙarfe 6 na yamma.

Ya bayyana cewa, kwale-kwalen ya kife ne a tsakiyar kogin yayin da yake jigilar fasinjoji zuwa garin Bagwai daga ƙauyen Badau.

Waɗanda lamarin ya rutsa da su sun mutu ne a cikin kogin saboda ba za su iya yin iyo zuwa gaɓar kogin ba kuma ba sa sanye da rigar ceto.