
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babban Sakataren Hukumar Gudanar da Tallafin Lafiya ta Jihar Bauchi (BASHCMA), Alhaji Ibrahim Ladan Duguri, ya rasu a hatsarin mota tare da ‘ya’yansa guda huɗu a yankin Yalwan Duguri da ke Ƙaramar Hukumar Alƙalerin jihar.
Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi, wanda ya tabbatar aukuwar lamarin, ya bayyana alhinin da jimam kan iftila’in, wanda ya auku a yammacin ranar Asabar. Ya bayyana mutuwar Alhaji Ibrahim Duguri a matsayin babban rashi ga Bauchi, musamman fannin lafiya, inda ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai sadaukarwa da jajircewa wajen inganta hanyoyin samun hidimar kiwon lafiya acikin al’umma.
A saƙonsa na ta’aziyya da Mai ba shi Shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Giɗaɗo ya fitar, gwamnan ya kuma bayyana alhininsa kan yadda al’amarin ya auku, yana mai isar da saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, Masarautar Duguri, abokai, abokan aiki da baki ɗaya al’ummar jihar kan rashin.
Haka kuma, ya yi addu’ar fatan samun lafiya ga Sulaiman, wanda ɗaya ne daga cikin ‘ya’yan marigayin ne da ya tsira yayin aukuwar lamarin.
Marigayin, wanda shi ne sakataren BASHCMA, ya taka muhimmiyar rawa wajen ciyar harkar kula da gudanarwar da tallafin lafiya gaba a jihar ta yadda al’umma, musamman marasa ƙarfi suke samun sauƙin samun magani. Sannan, sadaukarwarsa ta taimaka wa walwalar alhazan jihar musamman a lokacin da ake gudanar da harkokin aikin hajji a jihar da kuma ƙasar Saudiyya.
Kazalika, marigayin ya kasance babban amini kuma abokin karatun Gwamna Bala Mohammed baya ga nasarorin aiki da ya samu. A ƙarshe, gwaman ya yi addu’ar Allah ya jiƙan sa ya gafarta masa kurakuransa tare da ‘ya’yan nasa da kuma karɓar kyawawan ayyukansu, sannan ya sanya su a Aljannar Firdausi.


