Hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar ƙawayen amarya shida a Neja

Spread the love

Da yammacin Juma’ar da ta gabata hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla wasu matasa shida a kan hanyarsu ta rakiyar amarya a yankin Ƙaramar Hukumar Edita, Jihar Neja.

Shafin Tsalle Daya da ke Facebook ya ruwaito cewa, waɗanda lamarin ya shafa ƙawayen amarya ne su shida da kuma wani ƙanin ango ɗaya.

Ya zuwa haɗa wannan labari, babu wani bayani a hukumance game da hatsarin walau daga ɓangaren ‘yan sanda ko Hukumar Kiyaye Haɗurra daga yankin.

By Editor